Han Zheng: Sin za ta inganta hadin gwiwa da MDD, domin samar da adalci mai ma'ana a duniya
2024-01-31 11:13:09 CMG Hausa
Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya gana da shugaban babban taron MDD na 78 Dennis Francis a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
A jawabinsa yayin ganawar, Han ya bayyana cewa, a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na MDD, a ko da yaushe kasar Sin tana aiwatar da tsarin kasancewar bangarori daban-daban bil-hakki da gaskiya, da kiyaye iko da matsayin MDD. Ya kara da cewa, kasar Sin tana ba da shawarar tabbatar da daidaito, bisa tsari, da dunkulewar duniya, da ma tattalin arzikin duniya baki daya, wanda zai amfanar da kowa, tana kuma karfafa gwiwar dukkan kasashe, da su hada kai don fuskantar kalubale da samun ci gaba tare.
Ya bayyana cewa, shekarar 2025, shekaru 80 ke nan da kafuwar MDD. Ya ce a shirye kasar Sin take ta karfafa hadin gwiwa da MDD, tare da hada hannu da dukkan sassa, ta yadda za a kai ga kafa tsarin tafiyar da duniya mai adalci karkashin manufar gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama.
A nasa bangare Dennis Francis, ya bayyana kasar Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ta MDD, kuma mai taka rawa wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaban duniya. Yana mai cewa, yana sa ran kasar Sin za ta taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yayata manufar samun ci gaba mai dorewa, da ciyar da hadin gwiwar kasa da kasa gaba, gami da tunkarar kalubalen da duniya ke fuskanta. (Ibrahim Yaya)