logo

HAUSA

Yadda za a yi amfani da dabaru da fasahohin zamani wajen raya Ilimi a duniya

2024-01-31 10:26:37 CMG Hausa

An bude taron karawa juna sani na kasa da kasa game da amfani da dabaru da fashohi wajen raya ilimin zamani na shekarar 2024 a birnin Shanghai na kasar Sin. Ma'aikatar ilmi ta kasar Sin, da hukumar UNESCO dake kasar Sin da gwamnatin jama'ar birnin Shanghai ne suka shirya taron, wanda aka gudana daga ranakun 29 zuwa 31 ga watan Janairun 2024.

Kamar yadda sabon zagaye na juyin juya halin kimiyya da fasaha da masana'antu ke haɓaka, fasahar zamani ta ƙara zama karfin dake ingiza sauyi da sake fasalin tsarin tunani, tsare-tsare da hanyoyin aiki na al'ummar dan adam ta kowane fanni. Tsarin ya fito da sabbin ƙalubale da manyan damammaki don ƙirƙirar hanyoyi, da sake tsara fasali da haɓaka ci gaba. Aikace-aikace da haɓaka fasahar dijital sun yadu cikin dukkan sassan al'umma kuma za su yi tasiri mai zurfi kan ci gaban ilimin zamani a nan gaba.

Sama da mutane 800, da suka hada da baki sama da 400 daga ketare daga kasashe da yankuna sama da 70, ya zuwa yanzu sun yi rajistar halartar taron.

Majalisar dinkin Duniya, tare da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da dama, suna daukar matakai masu muhimmanci don ba da fifiko ga ilimin zamani a matsayin hanya mai muhimmanci da yunƙuri don tunkarar kalubale da samar da kyakkyawar makoma. 

Bayanai na nuna cewa, kasashe da dama sun aiwatar da dabaru don haɓaka fasahar raya ilimin zamani a matsayin wani muhimmin mataki na cimma wannan buri.

Manufar taron ita ce yin aiki tare da gwamnatoci,da jami'o'i,da makarantun firamare da sakandare, da kamfanoni, da sauran masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da abin ya shafa da ƙungiyoyi masu zaman kansu don yin hada gwiwa tare da habaka ayyuka da sabbin abubuwa a fannin ilimin zamani, ta yadda za a ci gaba da cimma burin ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.

Taken taron shi ne "Ilimin Dijital: Aikace-aikace, raba fasaha, da kirkire-kirkire", ana saran taron zai mai da hankali kan batutuwan da suka haɗa da Inganta Ilimin Dijital da Ƙwararrun malamai, Ilimin zamani da Gina rukunonin Koyo, ta yadda duniya za ta amfana da wannan sashe yadda ya kamata. (Yahaya/Ibrahim/Sanusi Chen)