logo

HAUSA

An kaddamar da kwamiti mai wakilai 37 da zai fito da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan gwamnatin Najeriya

2024-01-31 10:09:55 CMG Hausa

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da kwamiti mai wkailai 37 da zai yi duba tare da fito da sabon tsarin albashin da za a rinka biyan ma’aikatan gwamnatin kasar.

A lokacin da yake kaddamar da ’yan kwamitin a fadar shugaban kasa dake birnin Abuja, mataimakin shugaban na tarayyar Najeriya ya ce, yana da kyakkyawan fatan cewa rahoton kwamitin zai zamo masalaha ta karshe da za ta warware damuwar daukacin ma’aikatan Najeriya ta fuskar albashi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sanata Kashim Shettima ya ci gaba da cewa, batun albashi wani bangare ne kadan daga cikin sakayyar da gwamnati ya kamata ta rinka yi wa ma’aikata a sakamakon irin sadaukarwa da suke yiwa kasa a dukkan fanonin ci gaba. Ya yi fatan cewa ’yan kwamitin za su nuna adalci ga bangaren gwamnati da kuma na ma’aikata wajen gudanar da wannan aiki nasu ta hanyar fito da rahoton da zai zama karbabbe ka kowa.

“Matsayin da gwamnati za ta dauka bayan da ta nazarci rahoton da kuma gabatar mata shi ne za ta turawa majalissar domin ya zama doka.”

A sabo da haka mataimakin shugaban kasa ya bukaci membobin kwamitin da su hanzartar kammala aiki da aka ba su, tare da gabatar da rahotonsu ga gwamnati, kasancewar wa’adin da aka diba na amfani tsohon tsarin mafi kankantar albashi na naira dubu 30 zai kare ne a karshen watan Maris na wannan shekara, a don haka kammaluwar aikin kwamitin a kan lokaci shi ne zai baiwa gwamnati kwarin gwiwar hanzartar fara aiwatar da sabon tsarin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

A dai watan Maris na 2017 majalissar wakilan Najeriya ta yi gyara a kan dokar albashi ta kasa wanda ya wajabta sake duba hakkokin ma’aikata a dukkanin bayan shekaru biyar. (Garba Abdullahi Bagwai)