logo

HAUSA

Sin Na Ci Gaba Da Taka Rawa A Fannin Makamashi Mai Tsafta A Duniya

2024-01-31 19:44:35 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

Daya daga cikin bangarori da duniya ta karkata a halin yanzu shi ne, hanyoyin samar da makamashi mai tsafta, don biyan bukatun al’umma, da ma raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, a kokarin da ake yi na yaki da matsalar sauyin yanayi dake gurbata muhallin duniyarmu.

Yayin da wasu kasashe ke ci gaba da amfani da makamashin kwal, gas ko man fetur don biyan bukatunsu na makamashi, wadanda masana ke cewa suna gurbata muhalli, ita kuwa kasar Sin ta yi nisa wajen cimma manyan nasarori a fannin makamashi mai tsafta a duniya.

Babban manazarci a hukumar kula da makamashi ta duniya (IEA) Heymi Bahar ya bayyana cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin makamashin da ake iya sabuntawa, abin misali ne ga daukacin duniya.

A cikin rahoton shekara-shekara da hukumar IEA ta fitar a farkon wannan wata, ta lura cewa, duniya ta samu karin kashi 50 cikin 100 na karfin makamashin da ake iya sabuntawa a cikin shekarar 2023, fiye da na shekarar 2022, inda ta yi hasashen za a samu saurin bunkasuwa a shekaru biyar masu zuwa.

A fannin ci gaban da aka samu a fannin samar da wutar lantarki bisa hasken rana, kasar Sin ita kadai ta girka kusan na’urorin samar da wutar lantarki bisa haske da suka kai karfin 220GW, daidai da sauran kasashen duniya, wanda ya ninka saurinta a cikin shekara guda. Wannan ya kara nuna cewa, kasar Sin tana cika dukkan alkawuran da ta yi game da matakanta na raya makamashi mai tsafta, a kokarin da take yi na sauke nauyin dake bisa wuyanta a bangaren yaki da matsalar sauyin yanayin duniyarmu.

Masana na cewa, kasar Sin ta yi fice a matsayin kasar da ta fi kowace kasa a duniya samar da na'urorin samar da wutar lantarki bisa hasken rana na PV a duniya, inda ta ba da gudummawar kusan kashi 80 cikin 100 na masana'antun dake samar da irin wadannan na’urori a duniya.

Don haka, wannan wata dama ce ga kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa su koyi dabaru, da fasahohin da Sin din ta yi amfani da su wajen cimma wadannan nasarori, ta yadda ko dai su amfana da wadannan na’urori ko kuma su samar da wadanda za su dace da yanayin kasashensu. (Ibrahim Yaya)