logo

HAUSA

An yabawa tawagar ma’aikatan lafiya ta Sin dake aiki a DRC

2024-01-31 10:34:55 CMG Hausa

 

Mataimakin ministan lafiya na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Serge Emmanuel Holenn, ya bayyana tawagar jami’an lafiya ta kasar Sin a matsayin wadda ta taimaka wajen inganta kiwon lafiyar jama’a a kasar.

Serge Emmanuel Holenn ya bayyana haka ne yayin bikin tarba da ya gudana a Kinshasa domin maraba da kashi na 22 na tawagar jami’an lafiya Sinawa da kuma ban kwana da tawaga ta 21 da za ta kammala aikinta nan ba da jimawa ba.

Ya ce, a madadin gwamnatin kasar, yana bayyana godiya ga kasar Sin bisa yadda ta shafe shekaru sama da 50 tana tura jami’an lafiya kasar, yana mai bayyana kyakkyawan sakamako da daddadiyar hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce, a shekarun baya-bayan nan, tawagogin jami’an lafiya na kasar Sin, sun shawo kan kalubale irinsu Ebola da COVID-19, kuma sun taimaka wajen kare lafiyar dubban iyalai a kasar.

Mambobi 21 na tawaga ta 21 sun yi aiki a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo tsawon shekara 1, a asibitin abota ta Sin da Congo wato Sino-Congolese Friendship Hospital, dake Kinshasa da kuma babban asibin Haut-Katanga dake Lubumbashi. (Fa’iza Mustapha)