logo

HAUSA

Sojojin Sudan na ci gaba da fafatawa domin fatattakar dakarun RSF

2024-01-31 09:33:36 CMG Hausa

Babban kwamandan sojojin Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya bayyana cewa, sojojin kasar na ci gaba da yakin da suke yi na fatattakar dakarun samar da daukin gaggawa (RSF).

Al-Burhan wanda shi ne, shugaban rikon kwarya na kasar, ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga sojojin a wani sansanin soji da ke yankin New Halfa a gabashin kasar, yana mai cewa, burinsu shi ne ci gaba da tattaunawa.

Ya kuma yaba da irin goyon bayan da al'ummar Sudan suke ba sojojin, yana mai cewa, al'ummar Sudan da sojojin kasar, suna kan buri daya har sai an fatattaki wannan tawaye.

Ya kara da cewa, sojoji na ci gaba a yakin da suke yi na fatattakar ’yan tawayen RSF da ke samun goyon bayan jama'a da ba a taba gani ba. (Ibrahim Yaya)