logo

HAUSA

Sabon bincike ya alakanta lafiyar kwakwalwar iyaye mata da ta jarirai

2024-01-31 09:01:09 CMG Hausa

 

Wani nazari da masu bincike a jami'ar Curtin ta kasar Australiya suka jagoranta, ya gano alakar da ke tsakanin matsalar damuwa bayan haihuwa a masu juna biyu da matsalar saurin fushi a cikin 'ya'yansu.

Binciken, wanda aka wallafa a kwanakin baya, ya yi nazari kan gungun mata masu juna biyu 7994. Ya gano cewa, yaran iyaye matan da suka fuskanci alamun matsalar damuwa a lokacin da suke da juna biyu, sun ninka sau hudu, wanda daga bisani za a iya gano suna da matsalar taurin kai, ko ODD a takaice.

To, mene ne ma’anar ODD? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, ODD, lalurar dabi'a ce da ke tattare da taurin kai, da rashin biyayya, da kuma halin nuna kiyayya tun daga lokacin kuruciya ko samartaka. An yi kiyasin cewa, a wasu lokuta ana samun yaro 1 cikin yara 10 a Australiya da wannan cuta, inda ake hasashen wannan matsala, za ta iya ninkawa sau biyu a bangaren maza.

Marubucin binciken, Dr. Berihun Dachew na jami'ar Curtin ya nuna cewa, yayin da ake danganta matsalar bacin rai kafin haihuwa da wasu matsalolin kwakwalwa a cikin yara, a hannu guda kuma ba a tabbatar da hadarin cutar ODD a cikin 'ya'yansu ba.

Dr. Dachew ya kara da cewa, bincikensu ya yi nazari kan alakar dake tattare da matsalar damuwa kafin haihuwa kan yara masu lalurar ODD, a lokacin girma guda hudu: shekaru 7, 10, 13 da 15." Ya ci gaba da cewa, hakan ya baiwa tawagar damar lura da yadda yanayin ya ci gaba a tsakanin yara a tsawon shekaru.

Abin da suka gano shi ne, alaka ta kai tsaye kan abubuwan da ke haifar da matsalar damuwa a lokacin da kuma bayan mahaifiyar yaron ta haihu.

A cewar wani rahoton gwamnati da cibiyar kula da lafiya da walwalar jama’a ta Australiya ta wallafa, kusan 1 cikin iyaye mata 5, suna fama da wani nau'i na damuwa a lokacin da suke dauke da juna biyu da kuma bayan haihuwa, kuma matsalar ta fi kamari a tsakanin matasa da mata masu fama da matsalar tattalin arziki.

A karshe, binciken ya kara gabatar da dalili daya don ganowa da kuma magance matsalar damuwa da mata ke fama da ita.

Dachew ya ce, yana fatan karin yin nazari, zai iya samar da ingantattun magunguna da saurin magance matsalar damuwa ga matan da ke fama da irin wadannan alamomin damuwa, daga bisani kuma ‘ya’yansu na iya jin tasirinsa.

Saboda haka, a cewar Dachew, daukar mataki da samar da jinya cikin hanzari, suna da muhimmanci, kuma bincikensu ya yi karin haske kan muhimman abubuwa masu hadari game da ci gaban matsalar ta ODD da za a iya magancewa.