logo

HAUSA

Burkina Faso ta shiryawa duk wani abun da zai biyo bayan janyewarta daga ECOWAS

2024-01-30 10:57:15 CMG Hausa

Gwamnatin Burkina Faso ta ce za ta yi abun da ya kamata domin rage mummunan tasirin janyewarta daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS).

Ministan kula da harkokin wajen kasar Karamoko Jean Marie Traore ne ya bayyana haka jiya Litinin, a gidan talabijin na RTB na kasar.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Lahadi, kasashen Mali da Burkina Faso da Niger, suka bayyana janyewarsu daga kungiyar ta ECOWAS mai kasashe mambobi 15.

Da yake bayani game da tasirin hakan ga Burkina Faso, jami’in ya ce idan ana batun hadin gwiwar kasa da kasa, to dangantaka da ECOWAS ta kunshi hadin gwiwar bangarori daban-daban.

Amma ya ce Burkina Faso ta na da dadaddiyar dangantaka da kasashe makwabtanta, don haka akwai yiwuwar kara karfafa dangantakar. A cewarsa, zirga-zirgar mutane da kayayyaki cikin ‘yanci, shi ne babban kalubale. Kuma batu ne da ECOWAS ta yi aiki kansu na tsawon shekaru, don haka dole ne matakin janyewar ya yi tasiri a wannan bangare. Sai dai, ya ce akwai wasu dabaru da kasar za ta iya dauka domin cimma yarjejeniya da kasashe daban-daban kai tsaye. (Fa’iza Mustapha)