logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ta mutunta hurumin shari'ar Sudan

2024-01-30 14:53:31 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD, Dai Bing, ya bayyana yayin taron kwamitin sulhu, lokacin da yake nazarin batutuwan da suka shafi Sudan da kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa cewa, ya kamata kotun hukunta manyan laifufuka ta kasa da kasa ta ci gaba da martaba ka’idojin hadin gwiwa dake cikin yarjejeniyar Rome, kuma ta kasance ’yan baruwana da nuna adalci, mutunta ikon shari’a da shawarwari na Sudan, da kuma gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da Sudan.

Dai Bing ya kara da cewa, maido da zaman lafiya a Sudan, ya zama tushen tabbatar da adalci na shari’a. Ya kamata kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, ta mai da hankali kan zaman lafiya da kwanciyar hankali na kasar Sudan baki daya tare da taka rawar gani wajen warware matsalar Sudan yadda ya kamata. (Safiyah Ma)