Tashar jiragen ruwa ta Lekki ta zama abin misali na hadin gwiwar kasashen Sin da Najeriya
2024-01-30 16:00:27 CMG Hausa
A karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, kasashen Sin da Afirka sun samu sakamako masu yawa a hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu, inda aikin gina tashar jiragen ruwan Lekki ya zama abin koyi. Tashar Lekki dake Najeriya, wadda kamfanin kasar Sin ya zuba jari tare da gina ta, ita ce tashar jiragen ruwa mai zurfi ta zamani ta farko a Najeriya. A cikin shirinmu na yau, za mu ji me ya sa tashar jiragen ruwa ta Lekki ta zama abin misali na hadin gwiwar kasashen Sin da Najeriya.