logo

HAUSA

Guterres ya yi Allah wadai da rikicin kabilancin da ya yi sanadiyar mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiya biyu a yankin Abyei

2024-01-30 10:20:14 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da mummunan tashin hankali da ya barke a karshen mako a yankin Abyei da ake takaddama, inda aka kashe sojojin kiyaye zaman lafiya biyu tare da fararen hula da dama.

Stephane Dujarric, mai magana da yawun Guterres ya bayyana cewa, babban jamai’in na MDD ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankula da hare-haren da ake kaiwa dakarun wanzar da zaman lafiya, ya kuma yi kira ga gwamnatocin Sudan da Sudan ta Kudu, da su gaggauta gudanar da bincike kan hare-haren, tare da taimakon dakarun wanzar da zaman lafiya da aka fi sani da UNISFA, don ganin an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika a gaban kuliya. Ya kuma tunatar da dukkan bangarorin cewa, harin da aka kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD na iya zama laifukan yaki.

Dujarric ya ce, Guterres ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin kiyaye zaman lafiya da suka mutu daga kasashen Ghana da Pakistan, da fararen hula na Abyei da gwamnatoci da al'ummar Ghana da Pakistan.

Jami'ai a birnin Juba na Sudan ta Kudu sun tabbatar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, a kalla mutane 42 ne suka mutu sakamakon arangamar da ta barke tsakanin matasan al'ummar Twic masu dauke da makamai da kuma Ngok Dinka. (Ibrahim Yaya)