logo

HAUSA

Shugaban Masar da sakatare Janar na MDD sun yi kira da a ci gaba da samar da kudi ga ‘yan gudun hira Falasdinawa

2024-01-30 11:30:58 CMG Hausa

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da sakatare janar na MDD Antonio Guterres, sun jadadda bukatar ci gaba da samar da kudi ga hukumar MDD mai samar da agajin jin kai ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira (UNRWA).

Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya Litinin, shugaba al-Sisi da Antonio Guterres sun ce ci gaba da samarwa hukumar UNRWA kudi zai bata damar gudanar da ayyukanta na jin kai.

Zuwa ranar Lahadi, kasashen Canada da Australia da Birtaniya da Jamus da Italiya da Netherlands da Switzerland da Finland da Estonia da Japan da Austria da Romania, sun bi sahun Amurka wajen dakatar da samar da kudi ga hukumar UNRWA, bayan Isra’ila ta zargi wasu ma’aikatan hukumar da dama da hannu cikin harin da Hamas ta kai mata a watan Oktoban bara.

Wata sanarwa da fadar shugaban Masar ta fitar, ta ce tattaunawar tasu ta kuma tabo baki dayan yanayin yankin Gabas ta Tsakiya da hatsarin dake tattare da fadadar rikici a yankin. (Fa’iza Mustapha)