logo

HAUSA

Karamar jakadiyar Sin dake Legas ta halarci bikin saukar jirgin ruwan dakon kaya mafi girma a Najeriya a tashar Lekki

2024-01-30 21:02:25 CMG Hausa

A ranar 29 ga watan Janairu, aka gayyaci Madam Yan Yuqing, karamar jakadiyar kasar Sin dake Legas, don halartar bikin maraba da gabatar da jawabi a tashar ruwan Lekki, domin saukar jirgin ruwan dakon kwantena mafi girma a tarihin Najeriya.

Yan Yuqing ta bayyana a cikin jawabinta cewa, jirgin ruwan dakon kaya samfurin SCANDOLA dake amfani da makamashin iskar gas, shi ne jirgin ruwan dakon kaya mai daukar nauyin kwantena 15000, da ya taba zuwa tashar jiragen ruwa a Najeriya, wanda ke nuna wani muhimmin ci gaba a aikin tashar jiragen ruwa mai zurfin gaske ta Lekki.

Tashar jiragen ruwa mai zurfin ruwa ta Lekki wata babbar nasara ce da aka samu a aikin hadin gwiwa mai inganci na "shawarar ziri daya da hanya daya" tsakanin Sin da Najeriya, kuma kasar Sin ta yi farin cikin ganin ta taka rawar gani wajen zamanantar da Najeriya. (Yahaya)