logo

HAUSA

Kasar Sin ta ba Syria gudunmuwar kayayyakin sadarwa da darajarsu ta kai dala miliyan 10

2024-01-30 11:15:28 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayar da gudunmuwar kayayyakin sadarwa da darajarsu ta kai kimanin dala miliyan 10 ga kasar Syria, domin taimaka mata farfadowa da karfafa tashoshin sadarwa na kasar da yaki ya yi wa lahani.

An gudanar da bikin mika kayayyakin ne a jiya Litinin a babban birnin kasar, wanda ministan kula da harkokin sadarwa da fasaha na kasar Iyad Mohammad al-Khatib da jakadan Sin a kasar, Shi Hongwei suka halarta.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Sin a kasar ya fitar, ta ce za a yi amfani da kayayyakin a manyan tashoshin sadarwa na kasar 26 dake yankuna 4 da suka hada da karkarar Damascus da Aleppo da Hama da Deir al-Zour, domin samar da hidimomin intanet da na kiran waya ga iyalai sama da 100,000.

Ya kara da cewa, ana sa ran aikin kafa kayyayakin da kula da su, zai samar da guraben ayyukan yi kusan 1,000 a yankunan, lamarin da zai bunkasa tattalin arziki da rayuwar mazauna.

A nasa bangare, Iyad Mohammad al-Khatib ya ce gudunmuwar za ta taka muhimmiyar rawa wajen dawo da harkokin sadarwa a yankunan wadanda ke fama da ayyukan ta’addanci, haka kuma za ta bunkasa tattalin arzikin wuraren, ta wani bangaren ma, za ta saukaka aikin komawar ‘yan gudun hijira gidajensu. (Fa’iza Mustapha)