logo

HAUSA

An yiwa mutum na farko dashen kwakwalwa daga fasahar Musk

2024-01-30 14:51:29 CMG Hausa

Elon Musk ya fada, kamfaninsa ya yi nasarar dasawa mutum na farko na’urar zamani ta Neuralink a karon farko ranar Lahadi.

Musk ya bayyana a shafinsa na X, wanda ake kira Twitter a baya cewa, majinyacin yana murmurewa yadda ya kamata, kuma sakamakon farko ya nuna alamar gano sinadarin neuron a cikin kwakwalwar.

Kamfanin yana bunkasa fasahar dashen kwakwalwa, da nufin taimakawa marasa lafiya da ke fama da matsalar shanyewar bangaren jiki, ta hanyar sarrafa sassan jiki ta amfani da siginar jijiya kawai. (Ibrahim Yaya)