logo

HAUSA

An bayyana matsalar tsaro a matsayin abun dake kawo koma baya ga ci gaban harkokin noma a jihar Sokoto

2024-01-29 09:15:13 CMG Hausa

Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce, matsalolin tsaro na matukar shafar shirin gwamnati na wadata kasa da abinci a shiyyar Sokoto.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne lokacin da ya ziyarci ministan bunkasa harkokin noma na tarayyar Najeriya Abubakar Kyari a birnin Abuja, ya ce sama da rabin filayen noman dake jihar suna fuskantar barazanar ’yan ta’adda, lamarin dake hana manoma zuwa domin nomawa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Alhaji Ahmad Aliyu ya ce, duk da kokarin da gwamnatin jihar ke yi wajen wadata manoma da kayayyakin aikin gona da takin zamani tare da fadada filayen noman rani, amma yawan hare-haren ’yan ta’adda da ayyukan masu garkuwa da mutane yana sanyaya gwiwar manoman.

“Babban damuwarmu a jihar Sokoto a bangaren samar da abinci shi ne batun ayyukan ’yan ta’adda da ya shafi wasu sassan jihar, muddin babu tsaro manoma ba za su iya zuwa gona ba.”

Da yake jawabi, ministan bunkasa sha’anin noma na tarayyar Najeriya Alhaji Abubakar Kyari ya yaba matuka bisa kokarin da gwamnatin jihar ta Sokoto ke yi wajen kyautata sha’anin noma duk da wannan kalubale.

Ya kuma sanar da gwamnan cewa, “Gwamnatin tarayyar ta himmatu sosai wajen daukar matakai domin samun nasarar noman rani da na damuna masu zuwa musamman ma noman shinkafa da masara da kuma noman rogo, kuma domin ganin cewa an yi adalci wajen rabon tallafin kayan aikin gona ga manoma na hakika, gwamnatin tarayyar za ta hada kai ne da gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da sarakuna, da kungiyoyin masu zaman kansu da kungiyoyin manoma da kuma wasu hukumomin gwamnati domin dai cimma burin da aka sanya a gaba.” (Garba Abdullahi Bagwai)