logo

HAUSA

Kasashen AES da suka hada Burkina Faso, Nijar da Mali sun bayyana ficewarsu daga cikin kungiyar CEDEAO nan take

2024-01-29 09:24:30 CMG Hausa

A ranar jiya Lahadi 28 ga watan Janairun shekarar 2024 da yamma kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali suka fitar da wata sanarwa bi da bi domin bayyana matakin raba gari daga cikin kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta CEDEAO ko ECOWAS.

Wakilinmu Mamane Ada, daga birnin Yamai ya dubana wannan sanarwa da kuma abin da ta kunsa.

Ta gidan talabijin na kasa ne, kakakin kwamitin ceton kasa na CNSP, kanal manjo Abdourahamane Amadou ya karanta wannan sanarwa. Sanarwar na mai cewa, bisa burin dunkulewa tsakanin kasashen shiyya, bisa turbar tunanin zumunci, taimakon juna, hadin kai, zaman lafiya da ci gaba, tsoffin shugabannin kasashe kamar su janar Aboubacar Sangoule Lamizana na Haute Volta da yanzu take Burkina Faso, Laftana janar Seyni Kountche na Nijar da Janar Moussa Traoré na Mali suka yi tunanin kafa kungiyar yammacin kasashen Afrika CEDEAO a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 1975 tare da takwarorinsu na kasashe 12.

Bayan shekaru 49 da kafuwa, al'umomin kasashen Burkina Faso, da Mali da Nijar na ci gaba da lura cikin bacin rai, da rashin adalci na kungiyar da ke nisa da muhimman maradu da tunanin kishin Afrika da zaruman shugabannin dauri suka sanya gaba.

Haka zalika, wannan kungiyar yammacin kasashen Afrika ta zama ’yar amshin shatan kasashen yammacin duniya domin cin amanar kasashe mambobinta, da lamarin kawo barazana ga kasashen CEDEAO da kuma al'umomi nasu, da ke neman kawai jin dadi da kwanciyar hankali.

Haka kuma, kungiyar ba ta kawo dauki ba ga tsarin taimakon juna wajen yaki da ta'addanci da matsalar tsaro.

Abin haushi ma a cewar wannan sanarwa, a lokacin da wadannan kasashe uku suka yi niyyar daukar nauyin da ya rataya kan wuyansu, kungiyar ta dauki matakin ma kara jefa su cikin bala’i ta hanyar sanya musu takunkuman da suka saba wa dokoki da manufofin kungiyar a yayin da al'umomin kasashen suke fama da tashin hankali, kungiyar sai ta kara tsanantawa tare da sanya hannun wasu kasashen yammacin duniya.

Gaban wannan matsala, kaftan Ibrahim Traoré, birgadiye janar Abdrouhamane Tiani da kanal Assimi Goita a jere na kasashen Burkina Faso, da Nijar da Mali sun dauki babban nauyi gaban tarihi domin amsa bukatun al'umomin kasashen nasu, sun dauki nauyinsu bisa 'yanci na janyewa daga cikin kungiyar yammacin kasashen Afrika ta CEDEAO ba tare da bata wani lokaci ba.

Kasashen sun sanya hannu kan wannan sanarwa bi da bi a ranar 28 ga watan Janairun shekarar 2024 a birnin Ouagadougou, a birnin Bamako, da kuma a birnin Yamai. (Mamane Ada)