‘Yan mata biyu daga Afirka na kokarin cimma burikansu dake da nasaba da kasar Sin
2024-01-29 16:30:24 CMG Hausa
Wane buri ne mutum zai iya cimma a cikin shekaru takwas? Joy Nkiru Ikpeoha daga Najeriya ta samu digirin farko da na biyu kuma ta kafa kamfani a wadannan shekaru.
Ikpeoha, wadda aka haifa a shekarar 1992, ta je lardin Hainan dake kudancin kasar Sin a shekarar 2015, inda ta karanci harshen Sinanci a jami'ar Hainan. Shekaru hudu bayan haka, ta tsawaita karatunta na neman ilimi, inda daga karshe ta sami digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci a shekarar 2022.
Ikpeoha ta fara kasuwanci ne a wannan shekara, inda ta kafa kamfani a birnin Haikou, hedkwatar lardin Hainan, da nufin samar da ingantaccen tsarin hidima mai sauri ga kwararru ‘yan kasashen waje mabambanta.
"Aikin da nake yi a kamfanina shi ne taimaka wa kwararru ‘yan kasashen waje a Haikou ko Hainan wajen kafa kasuwancinsu, da kuma jin dadin zama a nan Hainan," a cewar Ikpeoha. Har ila yau, kamfanin na samar da wasu hidimomi ga baki na kasashen waje, ciki har da fassara da taimako wajen samun gidajen zama na haya.
Kwarewar Ikpeoha ta gudanar da kasuwanci ta samo asali ne a horan da ta samu a cibiyar raya basira ta duniya a birnin Haikou a lokacin da take karatun digirinta na biyu.
A cibiyar, ta kasance mai kula da taimaka wa 'yan kasashen waje halartar taro, kamar tarukan kasuwanci, cudanya, hadin gwiwa da kuma gabatar da ayyuka.
Ikpeoha ta ce, “ina jin kamar abin da na kware a kai ke nan. Don haka na yi tunanin ya kamata in sami kamfani na kaina don in sami cikakkiyar damar taimakawa 'yan kasashen waje da ba da hidima.”
Ikpeoha ta taki sa'ar cewa, godiya ga manufofin yankin cinikayya maras shinge na tashar jiragen ruwan Hainan wato Hainan Free Trade Port, ta samu damar fara kasuwancinta. Ta kara da cewa, wannan muhallin ya dace sosai ga matasa ‘yan kasuwa, musamman ma ‘yan kasashen waje wadanda ba su da makudan kudaden da za su kafa kamfanoninsu.
Hakika dai, Ikpeoha ta yi burin samun kamfani nata tun lokacin da ta fara karatun harkar kasuwanci, yanzu tana farin cikin cewa, burinta ya cika.
Ko da yake ba ta jima da fara kasuwancinta ba, Ikpeoha na da kyakkyawan fata game da makomar yunkurinta. Tana daukar damar da aikin raya yankin cinikayyar maras shinge na tashar jiragen ruwa ta Hainan ya bayar da muhimmanci, tana mai hasashen tasiri mai kyau ga kasuwancinta da kuma sauran al'ummomin kasashen waje dake Hainan.
Ikpeoha ta ce, “na yi imanin cewa, Hainan a nan gaba, za ta yi kyau, saboda yawancin baki sun fara zuwa nan." Ta kuma kara da cewa, suna kawo karin masu zuba jari daga ko'ina cikin duniya, har ma daga Afirka, kuma suna mai da hankali a kan harkar noma, yawon bude ido da sauran damammaki masu yawa.
Labarin kasuwancin Ikpeoha ya kawo ci gaba a gare ta. Ta bayyana cewa, “tun lokacin da na bude wannan kamfani, na gane cewa akwai karin abubuwa da zan koya, ko dai a aikace ko a ka'idance. Ina da sauran aiki a gaba na, kuma ina bukatar ci gaba da karin koyo. Akwai damammaki masu dimbim yawa a harkar.”
Duba ga duk shekarunta na zama a Hainan, Ikpeoha na daukar Hainan tamkar gidanta na biyu wanda ke da kwanciyar hankali da aminci. Baya ga harkokin kasuwancinta, Ikpeoha na harkar sadarwa a yanar gizo, wato ‘yar vlogger ce, tana ba da labari kan rayuwarta a Hainan, da abinci iri-iri, da abubuwan al'adu wadanda ke kawo mata farin ciki.
"Harshen Sinanci shi ne yaren da ke tashe a yanzu a duk fadin duniya. Harshen da ke ba da damammaki ga matasa, na gida da kuma na duniya baki daya," Asha Fum Khamis ce ta fadi hakan. Asha, wata malamar harshen Sinanci ce daga tsibirin Zanzibar na Tanzaniya, wadda ke koyar da harshen Sinanci a kwalejin Confucius ta jami'ar Dar es Salaam.
Da take bayyana ra'ayinta, malamar 'yar shekara 32 ta ce, “ina fatan kakannina da iyayena da 'yan uwana su koyi yaren Sinanci domin wannan shi ne mabudin samun aikin yi a kamfanonin kasar Sin dake aiki a Tanzaniya." Asha ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala koyar da Sinanci a kwalejin Confucius.
Asha wadda ta auri ‘dan kasar Tanzaniya mai jin Sinanci sannan kuma uwa ga dan watanni shida, cikin alfahari ta ce ta koyar da Sinanci ga dalibai sama da 300 ‘yan kasar Tanzaniya a tsawon shekaru uku da ta yi tana koyarwa. Asha ta ce, “kimanin dalibai 50 daga cikin fiye da 300 da na koyar sun dauki aikin koyar da harshen Sinanci, kuma wasu daga cikinsu sun samu guraben aikin yi a kamfanonin kasar Sin da ke Tanzaniya a matsayin tafintoci."
A yayin da take jaddada karuwar bukatar masu jin yaren Sinanci, Asha ta ce, kusan kowace rana, jami'ai daga kamfanonin kasar Sin dake aiki a Tanzaniya suna gabatar da bukatar neman 'yan Tanzaniya kwararrun a harshen Sinanci.
Ga kwalejin Confucius ta jami'ar Dar es Salaam, wadda ta cika shekaru 10 da kafuwa a watan Yulin shekarar 2023, ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta mu'amalar al'adu, da samar da sauki ga koyon harshen Sinanci, wanda ya ba da gudummawa sosai wajen inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Tanzaniya.
Kwalejin Confucius wadda aka kafa a shekarar 2013 bisa wata yarjejeniya da ta hada da jami'ar Dar es Salaam, da gidauniyar ilimi ta kasa da kasa ta kasar Sin, da kuma jami'ar koyar da ilmin da ke da nasaba da aikin koyarwa ta Zhejiang, da nufin zama babbar cibiyar nazarin harshen Sinanci da jarrabawa, a kokarin karfafa mu'amalar ilimi da al'adu a Afirka.
Asha ta ci gaba da cewa, ba a Tanzaniya da Afirka kadai ake matukar bukatar masu jin yaren Sinanci ba, har ma a duk fadin duniya inda kamfanonin kasar Sin ke aiki. Ta ce tuni ta fara koya wa jaririnta Sinanci, duk da cewa ba ta da tabbas ko yana fahimtar harshen.
Ba zato ba tsammani Asha ta fara sha'awar Sinanci a lokacin da take karatun aikin jarida a kwalejin watsa labarai ta Zanzibar a shekarar 2013, inda wata daliba ta yi tattaunawa da wata malamar Sinanci cikin harshen Sinanci zalla. Asha ta fara koyon Sinanci daga shekarar 2013 zuwa 2016, inda ta samu satifikit a fannin aikin jarida. Musamman ma, a shekarar 2015, ta zama zakara a matsayin wadda ta lashe gasar Sinanci baki daya, inda daga baya ta samu tallafin shiga gasar a kasar Sin.
Da take cin gajiyar tallafin da gwamnatocin kasashen Tanzaniya da Sin suka bayar, Asha ta yi kokarin neman samun digiri a fannin watsa shirye-shirye cikin harshen Sinanci a jami'ar sadarwa ta Zhejiang daga shekarar 2016 zuwa 2020. Bayan haka, kwalejin Confucius ta ba ta tallafin karatu na neman samun digiri na biyu a fannin aikin koyarwa a jami’ar koyar da ilmin da ke da nasaba da aikin koyarwa ta Harbin daga 2020 zuwa 2023.
Bayan Asha ta shiga kwalejin Confucius a matsayin malamar Sinanci a watan Nuwamba na shekarar 2021, yanzu tana aiki da kwalejin yawon bude ido ta kasa ta jami’ar Dar es Salaam. Ta yi hasashen kyakkyawar makoma ga bunkasuwar harshen Sinanci a Tanzaniya, inda ta yi hasashen samun karbuwarsa a tsakanin 'yan Tanzaniya, ciki har da yara kanana, cikin shekaru goma masu zuwa.
Asha ta ce, “Yayin da Tanzaniya ke nufin jawo hankalin masu yawon bude ido ta kasar Sin, dole ne mu koyar da yaren Sinanci ga ma'aikatanmu na cikin gida da za su yi hulda da Sinawa masu yawon bude ido. Makomar harshen Sinanci a Tanzaniya yana da kyau, nan da shekaru 10 masu zuwa, 'yan kasar Tanzaniya da dama ne za su yi magana da harshen Sinanci, ciki har da yara kanana."(Kande Gao)