logo

HAUSA

An gudanar da bikin sake bude ofishin jakadancin Sin a Nauru

2024-01-29 19:23:10 CMG Hausa

A yammacin yau Litinin ne aka gudanar da bikin sake bude ofishin jakadancin kasar Sin a Nauru a wani otel dake kudu maso gabashin kasar dake tsibirin Pasifik.

Ministan harkokin waje da cinikayya na Nauru Lionel Aingimea da Luo Zhaohui, shugaban hukumar raya hadin gwiwar kasa da kasa ta kasar Sin, wanda ya halarci bikin a matsayin wakilin gwamnatin kasar Sin, sun kaddamar da allon ofishin jakadancin kasar Sin.

Sin da Nauru sun rattaba hannu kan wata sanarwa tare a nan birnin Beijing a ranar 24 ga wata, kan batun maido da huldar dake tsakanin kasashen biyu a matakin jakadanci. (Yahaya)