logo

HAUSA

Batura kirar kasar Sin sun jawo hankalin kamfanoni daga duk fadin duniya

2024-01-28 20:14:34 CMG Hausa

“Babu wani kaya dake madadin kaya kirar kasar Sin”. Kwanan nan, kafar watsa labarai na Koriya ta Kudu, wato Korean Economy ya ba da rahoton matsalolin da kamfanonin kera motocin Koriya ta Kudu ke fuskanta dangane da wannan batu.

Yayin da kasar Amurka ke ci gaba da kara takunkumi a kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa ketare, kamfanonin motoci na Koriya ta Kudu da ke dogaro da kayayyakin batir na kasar Sin suna kokawa. Sakamakon haka, wadannan kamfanonin sun gabatar da ra’ayoyinsu na yin kira ga gwamnatin Amurka da ta sassauta abin da ake kira takunkumi kan kasar Sin, tare da ba su damar sayen muhimman kayayyakin batir daga kasar Sin.

A daya gefen duniya kuma, kamfanin Tesla na Amurka shi ma yana fuskantar irin wannan kalubale. Sakamakon dakushewar samar da batir na sabuwar motar lantarki ta Cybertruck, Tesla ya nemi tallafi cikin gaggawa daga masana'antun kasar Sin da fatan samun tallafin kayayyakin batir.

Daga kamfanonin Koriya ta Kudu zuwa kamfanonin Amurka, daga gwamnati zuwa 'yan kasuwa, dukkansu sun aike da sako iri daya, wato ba za a iya samar da motoci masu aiki da sabbin makamashi ba tare da kasar Sin ba.

Bayanai na baya-bayan nan da ma'aikatar masana'antu da sadarwa ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2023 yawan batir dake samar da makamashin lantarki da ake fitarwa a kasar Sin ya karu da kashi 87.1 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2022, kuma girman kasuwar ya kasance a kan gaba a duniya tsawon shekaru bakwai a jere. Haka kuma, kamfanonin kasar Sin sun kai guda 6 a cikin manyan kamfanonin batir 10 da ke samar da batura ga motocin makamashin lantarki a duniya.

Ci gaban masana'antar batir ta kasar Sin, ya sa kaimi ga bunkasuwar masana'antar kera motoci masu amfani da sabbin makamashi da karancin iskar carbon ta duniya. Wannan ya sa kokarin da wasu 'yan siyasar Amurka ke yi don cire batir din kasar daga tsarin samar da motocin masu amfani da makamashin lantarki ba zai kai ga nasara ba. (Yahaya)