logo

HAUSA

CMG ya kaddamar da biki kafin liyafar bikin bazara a New York

2024-01-28 15:41:15 CMG Hausa

A ranar 26 ga wannan wata, agogon birnin New York na kasar Amurka ne rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice ya kaddamar da wani biki kafin liyafar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin a birnin mai taken “Taya murnar bikin bazara na kasar Sin ta hanyar kallon liyafar bikin bazara na CMG”, domin ingiza cudanyar al’adu tsakanin kasa da kasa. Inda zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, da mataimakin babban sakatare kuma babban wakilin kawancen wayewar kan bil Adama na majalisar Miguel Moratinos, da sauran zaunannun wakilai ko ‘yan diplomasiyya na kasashen Amurka da Japan da Poland da Philippines da Malaysia da Vietnam da Cuba da Nicaragua da Mauritius dake wakilci a MDD, da jami’an sakatariyar majalisar, da abokan Sinawa da suka zo daga fannoni daban daban sama da 200 suka halarci bikin.

Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, bikin bazara bikin gargajiya mafi muhimmanci ne na al’ummar Sinawa, don haka al’ummu kaso 1 bisa 5 dake fadin duniya su kan taya murnar bikin ta hanyoyi daban daban. Kafin wannan, babban taron MDD karo na 78 ya zartas da wani kuduri, inda aka shigar da bikin cikin ranaikun hutawa na majalisar, lamarin da ya nuna cewa, ana kara mai da hankali kan wayewar kan al’ummar Sinawa, da kuma al’adun kasar. Kana Sinawa sun saba da kallon liyafar bikin bazara a jajibirin sabuwar shekara wato daren ranar karshe ta tsohuwar shekara. Kawo yanzu an riga an shirya liyafar bikin bazara sau 41 a jere, wadda ta kasance alamar al’adun kasar Sin.

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun shi ma ya yi tsokaci cewa, bikin bazara ya samo asalin ne a kasar Sin, amma al’ummun fadin duniya suna taya murnarsa tare. (Jamila)