logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat ya yi maraba da hukuncin da kotun kasa da kasa ya yiwa Isra'ila game da kisan kare dangi

2024-01-28 15:49:12 CMG HAUSA

 

Jiya Asabar, shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU Moussa Faki Mahamat ya yi maraba da hukuncin da kotun kasa da kasa ya yiwa Isra’ila game da kisan kare dangi da Afrika ta kudu ta gabatar, ya ce, wannan hukunci ya kare dokar kasa da kasa, dole ne Isra’ila ta kiyaye ka’idojin yarjejeniyar hana da kuma aiwatar da matakin kisan kare dangi ga wadanda suka aikata laifi.

A ranar 26 ga wata, kotun kasa da kasa mai hedkwatar birnin Den Haag na kasar Holland, ya yanke wannan hukunci kuma ya nemi Isra’ila da ta dauki matakin da ya dace don hana kisan kare dangi da matakan kyautata halin jin kai a zirin Gaza. (Amina Xu)