Babban jami'i: Dakatar da tallafi ga UNRWA yana haifar da hadari na siyasa da jin kai ga Falasdinawa
2024-01-28 16:01:25 CMG Hausa
Wani babban jami'in Falasdinu a jiya Asabar, ya bukaci kasashen da suka sanar da dakatar da tallafin da suke bai wa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu ta MDD wato UNRWA a takaice, da su sake duba shawarar da suka yanke don kaucewa hadarin siyasa da jin kai.
Babban sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar 'yantar da Falasdinu, Hussein Al-Sheikh, ya bayyana a dandalin sada zumunta na X cewa, "Muna da matukar bukatar tallafi ga wannan kungiya ta kasa da kasa, musamman a daidai wannan lokacin da Isra’ila ke ci gaba da fatattakar al'ummar Falasdinu."
A ranar Juma'a ne Amurka da Kanada suka sanar da dakatar da sabon tallafin da suke baiwa hukumar ta UNRWA na wucin gadi bayan da Isra'ila ta zargi wasu ma'aikatan hukumar ta MDD da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kaddamar a kudancin Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X, ministan harkokin wajen Isra'ila Yisrael Katz ya yabawa matakin da Amurka da Kanada suka dauka na dakatar da tallafin da ake baiwa hukumar ta MDD.
Kaza lika a ranar Asabar, kasar Austiraliya ta ba da sanarwar cewa za ta bi sahun Amurka da Kanada wajen dakatar da tallafin UNRWA. (Yahaya)