logo

HAUSA

Wang Yi Ya Tattauna Da Mashawarcin Shugaban Amurka Kan Tsaro

2024-01-27 21:36:14 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi wani sabon zagayen tattaunawa da mashawarcin shugaban kasar Amurka kan harkokin tsaro, Jake Sullivan a Bangkok na kasar Thailand.

A cewar Wang Yi, a bana ake cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka. Don haka ya kamata bangarorin biyu su dauki hakan a matsayin wata dama ta mutunta juna bisa daidaito da neman yanayi mai dacewa da za su yi hakuri da bambancin dake tsakaninsu. Kana ya kamata su mutunta muradun juna da yin zaman tare cikin lumana da hada hannu domin samun nasara tare, da zummar samar da hanyar da ta dace ta zaman jituwa tsakanin kasashen biyu.

Wang Yi ya kuma jaddada cewa, batun Taiwan, batu ne na cikin gida na kasar Sin, kuma zaben da aka yi a yankin, ba zai sauya matsayinsa na wani bangaren kasar Sin ba. Ya kara da cewa, ya kamata Amurka ta girmama manufar Sin daya tak a duniya da sanarwoyi 3 da kasashen biyu suka cimma, ta kuma nuna a aikace cewa ba ta goyon bayan ‘yancin Taiwan. Haka kuma, tana goyon bayan dunkulewar kasar Sin cikin lumana.

Har ila yau, Wang Yi ya bayyana cewa, bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa game da iyakar dake akwai tsakanin batun tsaron kasa da harkokin tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)