logo

HAUSA

Ghana za ta dage bukatar neman biza ga 'yan Afirka masu ziyara nan da 2024

2024-01-26 10:30:05 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya sanar da cewa, kasarsa na gab da aiwatar da manufar ba da izinin shiga kasar ga dukkan 'yan Afirka da ke son ziyartar kasar, ba tare da takardar biza ba, nan da karshen shekarar 2024.

Shugaba Akufo-Addo ya yi wannan alkawarin ne, a yayin bude taron ci gaban Afirka na shekarar 2024 da ya gudana a yankin Gabashin kasar, yana mai cewa, matakin ya yi daidai da manufofin yankin ciniki cikin 'yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA) na samar da kasuwar bai daya a nahiyar, a wani mataki na bunkasa tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi, da kawar da talauci.

Ya kara da cewa, gwamnatin Ghana ta himmatu wajen tabbatar da ganin dukkan ‘yan Afirka dake neman shiga kasar, sun yi haka ba tare da takardar biza ba. Yana mai cewa, akwai bukatar samar da irin wadannan tsare-tsare a fadin nahiyar, don saukaka zirga-zirgar jama'a, da kayayyaki, da ayyuka cikin 'yanci, ta yadda za a yi amfani da kasuwanci a matsayin hanyar sauya yanayin tattalin arziki a nahiyar Afirka.(Ibrahim)