Ya Kamata Sin Da Faransa Su Ba Da Jagora Wajen Yin Mu’amala A Shekaru 60 Masu Zuwa
2024-01-26 20:19:00 CMG Hausa
Jiya Alhamis 25 ga wata ne a babban dakin wasan kwaikwayon kasar Sin da ke nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar, aka nuna wasan kwaikwayon wake-wake mai suna Romeo da Juliet, wanda mai tsara kide-kide na kasar Faransa Charles Francois Gounod ya samar da shi. Masu fasaha na Sin da Faransa sun nuna wasan mai kayatarwa ne cikin hadin gwiwa, wasan da ya kasance kyautar musamman ta murnar cika shekaru 60 da kulla huldar jakadanci a tsakanin kasashen 2.
Yayin da kasar Sin ke mu’amala da kasashen yammacin duniya, Faransa ta sha bamban sosai, inda ta zama ta farko tsakanin manyan kasashen yammacin duniya da suka kulla huldar diplomasiyya da jamhuriyar jama’ar kasar Sin a hukumance, kana ta zama ta farko tsakanin manyan kasashen yammacin duniya da suka kyautata hulda da Sin zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni da kuma tattaunawa da Sin dangane da manyan tsare-tsare.
A yayin liyafar da aka gudanar ta murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Faransa a daren jiya, shugabannin kasashen 2 sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo, inda shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, tarihin musamman na huldar da ke tsakanin Sin da Faransa ya samar da ruhin Sin da Faransa mai ‘yancin kai, fahimtar juna, yin hangen nesa, moriyar juna da samun nasara tare. Ya kuma gabatar da shawarwari 4 dangane da zurfafa hadin gwiwar kasashen 2 a nan gaba, wato wajibi ne Sin da Faransa su tsaya kan raya huldarsu da habaka yin mu’amalar al’adu da kara azama kan cudanyar al’umma da yin kirar raya duniya mai sassa daban daban kuma mai adalci da tsari da oda, da bunkasar tattalin arzikin duniya mai kunshe da kowa da amfanawa kowa, da kuma nacewa kan samun moriyar juna da nasara tare. Xi ya gabatar da wadannan shawarwari 4 ne domin neman kare muradun bai daya na Sin da Faransa, da kokarin kara sauke nauyi dake wuyansu tare a duniya, shawarwarin da suka tsara manufar raya huldar da ke tsakanin Sin da Faransa a shekaru 60 masu zuwa.
Sin da Faransa na da kujerun din din din a kwamitin sulhu na MDD, kuma kasashe ne masu kishin zaman lafiya da kin yarda da nuna kiyayya tsakanin rukunoni, da kuma rungumar manufar cudanyar sassa daban daban. A cikin duniyar da ke fama da tashin hankali, kamata ya yi Sin da Faransa su kara hada kansu, su daidaita matsalolin tafiyar da harkokin duniya tare, su kuma taimaka wajen kwantar da kura a duniya. (Tasallah Yuan)