logo

HAUSA

Kasar Rasha ta bukaci a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD bayan harbo jirgin sama

2024-01-25 11:05:51 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrov ya bayyana jiya Laraba cewa, kasar Rasha ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, bayan harbo jirgin Rasha dauke da sojojin Ukraine da aka kama.

A wani taron manema labarai a hedkwatar MDD da ke New York, Lavrov ya ce Moscow ta bukaci a gudanar da taron da karfe 3 na rana, na jiya Laraba agogon New York. Amma a hakika ba a tsara taron yadda ya kamata ba.

Lavrov ya ce an harbo wani jirgin saman Rasha kirar IL-76 tare da jami'an sojan Ukraine 65 da aka kama a cikinsa da jami'an Rasha uku da ma'aikatan jirgin su shida.

Lavrov ya ce makami mai linzami na tsaron sama da Ukraine ta harba daga yankin Kharkiv ne ya kabo jirgin a yankin Belgorod. Jirgin na IL-76 na dauke da kamammun sojojin Ukraine 65 daga Moscow zuwa Belgorod domin yin musanyar fursunonin da aka amince tsakanin Moscow da Kiev. (Yahaya)