logo

HAUSA

Wasanni da ake shiryawa a kauyukan Sin na samun karbuwa ga sassan kasa da kasa

2024-01-25 21:27:10 CMG Hausa

Kusan shekara daya da ta gabata, ba a san gundumar Rongjiang dake lardin Guizhou, na kudu maso yammacin Sin sosai ba. Amma a yanzu, gundumar Rongjiang ta fito da kan ta a idanun duniya ba a Sin kadai ba, har ma da sauran sassan ketare, albarkacin gasar kwallon kafa da ake shirya a wurin.

Ana dai shirya wannan gasa ne ta kwallon kafa wadda ake yiwa lakabi da "Cun Chao", tsakanin al’ummun yankin ba tare da la’akari da kwarewa ba. "Cun Chao" na nufin gasar kwallon kafa ta kauye ko "Village Super League." a turance. A lokacin bazara da ya gabata, Cun Chao ta samu karbuwa da ba a yi tsammani ba, inda adadin masu kallon gasar ya haura mutum 10,000.

Baya ga gasar kwallon kafa ta kauye wato Cun Chao, akwai kuma gasar kwallon kwando da kwallon raga ko “volleyball” dake samun karin karbuwa ga sassan kasar Sin, har ma gasannin sun ja hankalin hukumar shirya gasar kwallon kwando ta kasa da kasa wato NBA, da gasar Firimiyar Ingila, wadanda suka turo wakilan su domin ziyara da duba yiwuwar gudanar da hadin gwiwa.

Karbuwar wasannin kauyuka

Daga ranar 13 ga watan Mayu zuwa 29 da watan Yuli da suka gabata, Cun Chao ta hallara kungiyoyin wasa daga kauyuka 20, inda suka fafata a wasanni 98. Wannan gasa ta samu ‘yan kallo sama da miliyan daya, da masu bibiyarta ta yanar gizo sama da miliyan 50.

Me yasa gasar Cun Chao ta fita daban?

Sabanin gasannin ajin kwararru, kamar gasar kwallon kafar kwararru ta kasar Sin, ita gasar Cun Chao tana da tsari mai sauki, inda ‘yan wasan ta ke fitowa daga sassa daban daban. A filin wasa suna taka leda tamkar taurarin kwallo, amma a fagen rayuwa, wasun su masu sana’un hannu ne, wasu direbobi, wasu dalibai har ma da mahauta. Ana kuma sanya kyautar naman alade, ko na tumaki, ko kaji bisa gwargwadon bukata.

Baya ga kasancewar ta gasar kwallon kafa, Cun Chao na wakiltar nuna al’ada. Yayin da ake hutun rabin lokaci, kauyawa na sanya tufafin gargajiya irin na kabilun su, suna rera wakoki da raye rayen gargajiya, wanda hakan ke samar da wani yanayi na shagalin biki.

Bisa tsarin ta na gasa mai kunshe da wasa da nuna al’adu, Cun Chao ya haifar da gajiya ta fuskar tattalin arziki ga mazauna gundumar Rongjiang. Yayin gasar, masu sayar da albarkatun gona dake wurin, sun sayar da kayan da suka kai yuan miliyan 401, kana adadin abinci da ake ci da dare a yankin yayin gasar ya karu da kaso 362.5 bisa dari a shekara, inda ya kai yuan miliyan 309, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 43.5.

A kauyen Taipan, inda aka gudanar da wasan karshe na gasar kwallon kwando ta “Cun BA”, wato kauyen gasar kwallon kwando, masu zuwa yawon bude ido sun yi matukar karuwa, inda otal da gidajen cin abinci ke cika da jama’a a kullum, lokacin da ake gudanar da gasar. Masu sayar da shinkafa, wadda daya ce daga kyautukan da ake bayarwa a gasar, sun samu karin ciniki da ninki sama da 10 cikin shekara guda.

A cewar Yang Dezhao, shugaban gundumar Taijiang "Bukukuwan raya al’adu da wasanni da ake gudanarwa a nan, sun bunkasa ci gaban sashen yawon bude ido a gundumar Taijiang".

A shekarar 2022, gundumar ta karbi ‘yan yawon bude ido sama da miliyan 1.5, inda ta yi nasarar tara kudin shiga da ya kai yuan biliyan 1.8, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 251.9. Cikin rubu’i 3 na farkon shekarar 2023, adadin masu zuwa yawon shakatawa da kudaden da aka samu sakamakon hakan sun karu da kaso 60 bisa dari, da kuma kaso 92 bisa dari a shekara.

Wadannan sauye-sauye na wakana a kauyuka daban daban na kasar Sin. A watan Satumban bana, gasar kwallon kwando da aka shirya a kauyen Liaoyuan, na lardin Jilin dake arewa maso gabashin kasar Sin ya hallara masu kallo har mutum 10,000.

A garin Xinglong na birnin Guyuan karkashin jihar Ningxia ta Hui mai cin gashin kai dake arewa maso gabashin Sin, an shirya gasar kwallon kwando a waje ta mutane 30,000, da kuma ta rufaffen wuri da ake yi bayan karfe 6 na yammacin ko wace rana.

Har ila yau, a gundumar Nan ta lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin, an shirya wata gasar ta kwallon kwando, da kwallon raga ta “volleyball”, da gasar “badminton” mai hade da wasu wasannin gargajiyar yankin mai dausayi, wadda ita ma ta hallara sama da masu kallo 100,000 yayin hutun ranar kafuwar kasa, wato “China's National Day” da ta gabata.

A cewar Wang Xueli, daraktan cibiyar bincike da raya wasanni a jami’ar Tsinghua "A tsari na birane ko kauyuka, wasanni na taka karin rawar gani wajen samar da ci gaba. Wasanni na dinke jama’a da birane waje guda, suna kuma hada kan mutane da kauyuka. Wannan na nuni ga ci gaban da ake samu a fannin raya kauyuka”.

Karbuwa daga sassan kasa da kasa na bunkasa musaya

A matsayin wani sabon salo na ci gaba, gasannin kauyukan Sin na dade janyo hankulan sassan kasa da kasa. A watan Satumba, gasar Cun Chao da gasar kwallon kafa ta Firimiyar Ingila sun kulla yarjejeniyar hadin gwiwa, yayin baje kolin harkokin ba da hidima na Beijing na shekarar 2023, a wani mataki na yayata kwallon kafa a matakin kasa, tare da dunkule fannin da harkokin musayar al’adu.

A ranar 12 ga watan Disamba da ya gabata, gasar Firimiya ta Ingila ta kaddamar da shirin samar da kwarewa a gundumar Rongjiang, inda manajan wasan kwallon kafa dan Birtaniya Warren Leat, ya jagoranci kwas din bayar da horo na yini 4 ga masu horas da ‘yan wasa 44 dake yankin.

Game da hakan, jami’in lura da harkokin watsa labarai da tallace-tallace na hadin gwiwar Sin da gasar Firimiyar Ingila Hu Zhaoheng, ya ce "Ina fatan za a samu karin tattaunawa a matakin farko tsakanin Sin da Ingila a nan gaba".

Ko ma dai mene ne makoma, hadin gwiwar gasar Cun Chao da firimiyar Ingila, ya nuna kyakkyawan mafari na kawar da shinge, tare da samar da gadar musayar al’adu mabanbanta.

Kaza lika, a filin wasan kwallon kwando, taurarin wasan na NBA Jimmy Butler, da Allen Iverson, da Stephon Marbury, dukkanin su sun ziyarci kauyen Taipan a lokacin bazara. Sun buga wasa tare da mutanen wurin da kuma yara kanana, sun yi cudanya da ‘yan kallo, sun rera wakoki tare da mazauna wurin, kana abu mafi muhimmanci sun kalli wasan kwallon kwando da mazauna wurin suka buga.

A tsokacin da ya yi game da hakan, Stephon Marbury ya ce "Na yi farin cikin zuwa nan. Mutanen wurin sun fito da sunayen su da sunan kasar Sin ga duniya. Kwazon su da sha’awar su ya sha banban da na Amurkawa, duba da cewa, ban taba buga wasa a gaban jama’a mai yawan wannan a wuri budadde ba. Na tabbatar gasar Cun BA tana kara inganta, ina kuma burin ganin na zama bangare na wannan gasa".

A watan Satumba, jaridar “Washington Post” ta wallafa wata Makala mai taken: Gasar kwallon kwando ta kauye, na iya zama sabon wasan kwallon tebur da ka iya dinke alakar Amurka da Sin".

Game da hakan, karamin darakta a cibiyar Jack D. Gordon ta tsara manufofin ci gaban al’umma, karkashin jami’ar Florida International, mista Leland Lazarus, ya rubuta wata makala mai lakabin “Yadda kwallon kwando ke zama wata gada ta sada matasan Amurka da Sin da juna”.

A cewar Lazarus, "Kwallon kwando za ta iya samar da wata gada tsakanin matasan Amurka da na Sin".

Wata dadaddiyar jumla ta Sinanci na cewa “Alakar kasashe biyu na dogara ne kan kaunar juna tsakanin al’ummun su”, don haka mai yiwuwa ne ‘yan wasan Amurka da na Sin za su zamo abokai a filin wasan kwallon kwando, kana su bunkasa kawancen su zuwa teburin tattaunawa. Kwarewar da za su samu ta fuskar cudanyar wasanni na iya zama tubalin gina hadin gwiwa".