logo

HAUSA

Afirka da ke kudu da hamadar Sahara ta fuskanci yawan mutuwar masu ciki da iyaye mata da jariransu a shekarar 2020

2024-01-25 16:13:36 CMG Hausa

 

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO da wasu hukumomin MDD sun kaddamar da rahoto tare a kwanan baya, inda suka nuna cewa, a shekarar 2020, mace 1 tana mutuwa sanadiyar samun ciki ko haihuwa a cikin ko wadanne mintuna 2 a duniya. Kana an samu mutuwar masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba da yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Wannan rahoton mai taken “hasashen yawan mutuwar masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba” ya yi nuni da cewa, masu nazari sun bibiyi mata masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba da suka mutu daga shekarar 2000 zuwa ta 2020 a duk duniya. Rahoton ya yi kiyasin cewa, masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba kimanin dubu 287 sun rasa rayukansu a shekarar 2020 a duk fadin duniya, adadin da ya dan ragu bisa dubu 309 a shekarar 2016, lokacin da aka fara kokarin cimma manufar MDD ta samun ci gaba mai dorewa.

An samu wadannan mace-mace ne a yankuna mafiya fama da kangin talauci da kasashen da ke fama da tashin hankali. A shekarar 2020, an samu mutuwar masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba da yawansu ya kai kashi 70 cikin 100 a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. A cikin kasashe 9 da mummunar matsalar lafiyar jiki ta shafa, masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba 551 cikin 100 ne suka mutu, matsakaicin adadi a duniya shi ne 223.

Muhimman dalilan da suka haifar da mutuwar masu juna biyu da iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba, su ne, zubar jini da yawa, ciwon hawan jini, kamuwa da kwayoyin cuta sakamakon samun ciki, kamuwa da cututtukan da suka biyo bayan zub da ciki ta hanyar yin tiyatar gaggawa da dai sauransu, wadanda galibinsu ake iya yin rigakafi da ma shawo kansu.

Jami’an hukumar WHO sun nuna cerwa, kamata ya yi hukumomi masu ruwa da tsaki su gaggauta zuba jari kan gudanar da shirin kayyade yawan haihuwa, da cike gibin da ke akwai na karancin ma’aikatan lafiya dubu 900 a duniya. Haka kuma, akwai bukatar hukumomi masu ruwa da tsaki su tabbatar da bai wa mata hidimomin kiwon lafiya kafin da kuma bayan haihuwa. (Tasallah Yuan)