logo

HAUSA

’Yan tawayen Houthi na Yemen sun dauki alhakin kai hari kan jiragen ruwan Amurka

2024-01-25 11:40:36 CMG Hausa

Jiya Laraba, kakakin kungiyar Houthi ta Yemen Yahya Sarea ya sanar da cewa, a wannan rana, ’yan tawayen kungiyar sun kai hari kan jirgin ruwan soja da jirgin ruwan kasuwanci na kasar Amurka a wuraren dake kusa da mashigin tekun Aden da mashigin tekun Bab El-Mandeb.

Ya kuma kara da cewa, a wannan rana, ’yan tawayen Houthi sun yi musayar wuta da jiragen ruwan soja na kasar Amurka, wadanda suke kiyaye jiragen ruwan kasuwancin Amurka guda biyu. Makamai masu linzami da ’yan tawayen Houthi suka harba sun halaka jirgin ruwan Amurka guda daya kai tsaye, sa’an nan, jiragen ruwan kasuwancin guda biyu sun koma wurin da suka fito, ba su shiga Bahar Maliya, wato Red Sea ba.

Kuma sanarwar da rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta fidda a ranar 24 ga wata, ta nuna cewa, a wannan rana da yamma, ’yan tawayen Houthi sun harba makamai masu linzami guda uku kan jiragen ruwan kasuwanci dake rataye da tutar kasar Amurka da suka doshi mashigin tekun Aden. Kana, jiragen ruwan sojan kasar Amurka sun cimma nasarar tsare biyu daga cikinsu, na uku kuma ya fadi cikin teku. Kuma, ba wanda ya ji rauni ko rasa rai cikin jiragen ruwan kasuwanci, kuma babu asarar jirgin ruwa. (Maryam)