logo

HAUSA

Babban jami’in MDD ya yi kira da dauki matakin gaggawa don yaki da ta’addanci a Afirka

2024-01-25 10:50:23 CMG Hausa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a ranar Laraba ya jaddada wajibcin yaki da ta’addanci da ke kara ta’azzara a Afirka, yana mai bayyana halin da ake ciki a matsayin “hatsari a fili kuma a halin yanzu” ba ga nahiyar kadai ba har ma ga duniya.

“Yanzu wannan gini, da kungiyarmu suna wakiltar manufofin bil’Adama mafi girma, wadanda suka hada da zaman lafiya, tattaunawa, ci gaba, ‘yancin dan Adam da hadin gwiwa, yayin da ta’addanci ke wakiltar kishiyar wadannan manufofin, a cewar babban magatakardan a cikin wani jawabinsa a taron yaki da ta’addanci na duniya a hedikwatar MDD dake birnin New York.

Babban jami'in na MDD ya jaddada muhimmancin ci gaba mai dorewa, gami da kare hakkin bil'Adama a matsayin muhimmin matakin yaki da ta'addanci.

A cikin tunatarwarsa game da yadda mutane ke rasa rayukansu sakamakon ta’addanci, babban sakataren ya yi tsokaci kan halin da mata da ‘yan mata ke ciki, wadanda galibi su ne na farko kuma mafi muni da matsalar ke shafa, inda ya buga misali da Najeriya da Iraki. Yana mai nanata bukatar dabarun yaki da ta'addanci domin ba da fifiko ga hakkin dan adam. "Ba za mu iya yakar ta'addanci ta hanyar maimaita irin wannan musantawa ba." (Yahaya)