logo

HAUSA

Abin Mamaki! Yawan Motocin Da Sin Ta Samar Kuma ta Sayar Ya Zarce Miliyan 30

2024-01-24 16:24:19 CMG HAUSA

Abokai, yau ina son bayyana muku wani abin a zo a gani a nan kasar Sin.

A shekarar 2009, yawan motocin da Sin ta samar kuma ta sayar ya zarce miliyan 10, adadin da ya fi Amurka yawa, abin da ya alamanta cewa, Sin ta zama kasar da ta fi yawan samar da sayar da motoci a duniya, kuma kawo yanzu Sin ta kiyaye wannan matsayi a cikin shekaru 15 a jere. Wadannan alkaluma sun bayyana ci gaba mai armashi a bangaren masana’antun samar da motoci, da ma ingantacciyar kasuwar Sin.

Sai kuma a kwanan baya, kungiyar masana’antun samar da motoci ta kasar Sin ta samar da kididdigar da ke shaida cewa, a shekarar 2023, a karon farko ne yawan motocin da Sin ta samar kuma ta sayar ya haura miliyan 30, wanda hakan ya kai wani matsayin koli a tarihi. Daga cikinsu, yawan motocin da ta fitar zuwa waje ya kai miliyan 4.91, har ana sa ran za ta zama kasar da ta fi yawan fitar da motoci zuwa ketare.

Daga kasar da ta fi yawan samar da sayar da motoci a duniya, zuwa   mai jira gadon matsayin kasa mafi yawan fitar da motoci zuwa ketare, lamarin ya bayyana yadda kasashen duniya suka yi na’am da masana’antun kasar Sin, da ma ingantaccen tattalin arzikin kasar Sin da boyayyen karfinta.

Abokai, daga cikin motocin da kuke gani na yau da kullum, nawa aka shigo da su daga kasar Sin?(Mai tsara bidiyo da rubutu:MINA)