Amurka ta kai hare-hare kan mayakan da ke samun goyon bayan Iran a Iraki
2024-01-24 11:11:29 CMG Hausa
Rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta sanar da cewa, dakarun Amurka sun kai hare-hare na bai daya kan wasu wuraren da wata kungiyar sa-kai da ke samun goyon bayan Iran ke amfani da su a Iraki.
Sanarwar da CENTCOM ta wallafa a shafin X ta ce, da misalin karfe 12:15 na safiyar Laraba agogon kasar Iraki ne aka kai hare-haren kan wasu cibiyoyi guda uku da kungiyar mayakan sa-kai ta Kataib Hezbollah (KH) da sauran kungiyoyin da ke da alaka da Iran ke amfani da su a Iraki,
“Wadannan hare-haren sun shafi hedkwatar KH ne, da ma’ajiya, da wuraren horo na makaman roka, da makami mai linzami, da kuma motoci marasa matuka masu kai hari”, a cewar rundunar ta kasar Amurka. (Yahaya)