logo

HAUSA

Shugabannin Masar da Rasha sun aza harsashin kafa sabon sashen tashar makamashin nukiliya

2024-01-24 11:21:12 CMG Hausa

A jiya Talata, shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun halarci bikin kaddamar da aikin gina wani sabon sashen tashar makamashin nukiliya ta El-Dabaa ta kafar bidiyo.

Al-Sisi ya ce shirin nukiliyar Masar na lumana zai ba da gudummawa wajen samar da makamashi mai aminci, da arha, kuma na dogon lokaci, tare da rage dogaro da makamashin mai da kwal da iskar gas, da kuma gujewa matsalar sauyin farashinsu.

A nasa bangaren, shugaban na Rasha ya jaddada cewa Masar kawa ce kuma abokiyar huldar Rasha, ya kara da cewa dangantakar kasashen biyu ta ginu ne bisa daidaito da mutunta juna.

A watan Yulin shekarar 2022 ne Masar ta fara aikin gina tashar nukiliyar El-Dabaa, tashar makamashin nukiliya ta farko a kasar, wadda ke lardin Matrouh na tekun Bahar Rum, mai tazarar kilomita 300 daga arewa maso yammacin Alkahira babban birnin kasar. (Yahaya)