logo

HAUSA

Kalamai marasa kyau a MDD ba za su hana mutane su fahimci ainihin Xinjiang ba

2024-01-24 21:27:56 CMG Hausa

Jiya Talata ne a birnin Geneva na kasar Switzerland, yayin da take halartar taron bita na hudu na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, kasar Sin ta gabatar da tsarin raya hakkin dan Adam da kuma nasarorin da ta cimma. Fiye da kasashe 120 sun furta kalamai masu kyau. Wannan ya kawo cikas ga wasu tsirarrun kasashen yammacin duniya wadanda suka yi kokarin siyasantar da batun nazarin kare hakkin dan adam ta hanyar wasu batutuwa irin su jihar Xinjiang ta kasar Sin. Har ila yau, a jiyan kasar Sin ta fitar da wata farar bayani mai taken "Tsarin shari'a da kuma ayyukan yaki da ta'addanci na kasar Sin", wanda ya yi cikakken bayani kan ayyukan yaki da ta'addanci da kasar Sin ta samu.

Masanan da abin ya shafa sun ce, idan aka yi la’akari da abin da wannan takarda ta kunsa, za a fahimci cewa, yaki da ta’addanci kamar yadda doka ta tanada a ko’ina, ba wai kawai yakar ta’addancin da ke jefa rayuka da dukiyoyin jama’a cikin hadari ba ne, har ma yana kare hakkin jama’a na rayuwa, samun ci gaba da sauran hakkokin da suka shafi bil-Adama.

Ta'addanci abokin gaba ne na bil-Adama, kuma kasar Sin ta yi fama da wannan matsala. Tsoro, hasarar rayuka, ci gaba, wadannan sakamakon sun bayyana a fili cewa, yaki da ta'addanci bisa doka ne kawai zai iya kare hakkin bil-Adama. Ruhin bin doka da oda a yaki da ta'addanci na kasar Sin, ya yi daidai da ka'idoji da ra'ayoyin yaki da ta'addanci na kasa da kasa. Ba wai kawai ya hana da hukunta ayyukan ta'addanci yadda ya kamata ba, har ma da mutuntawa da kare hakkin dan Adam yadda ya kamata. Wasu kasashen yammacin duniya, suna amfani da "ma'auni biyu" wajen yaki da ta'addanci da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin, ta hanyar fakewa da batun "doka" da "yancin dan Adam", wanda ba wai kawai yana kawo cikas ga hadin gwiwar yaki da ta'addanci na kasa da kasa ba, har ma da gurgunta hadin gwiwar kare hakkin dan Adam na duniya. (Ibrahim)