logo

HAUSA

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara…

2024-01-24 16:59:50 CMG Hausa

Bunkasuwar kasar Sin ba ta taba zama wata barazana ko kalubale ga duniya ba, sai ma hakan ya kasance muhimmiyar dama ga duniya baki daya. Sanin kowa ne cewa, misali, kasar Sin ta raba fashohinta na yaki da talauci da kwararowar hamada da yaki da ta’addanci bisa doka da rage fitar da gurbatacciyar iska mai illa ga muhallinmu da sauran fannoni ga kasashen duniya.

Idan ba a manta ba, a lokacin da aka samu bullar annobar COVID-19 a sassan duniya, an ga yadda mahukuntan kasar Sin suka rika raba fasahohi da kayayyakin yaki da annobar da ma ma’aikatan kiwon lafiya zuwa sassan duniya, don yakar annobar. Haka kuma a lokacin da ta yi nasarar samar da alluran riga kafin annobar COVID-19, kasar Sin ta raba alluran ga kasashen duniya, matakin dake kara tabbatar da cewa, bunkasuwar kasar Sin ba barazana ko kalubale ne ga duniya ba. Wata muhimmiyar dama ce ga duniya.

Bangaren kasar Sin dai ya sha nanata wannan batu a mabambantan lokuta, tare da nuna misali a zahiri, ko da a baya-bayan nan ma, duniya ta ga yadda motoci masu aiki da wutar lantarki da kasar ta kera, suke samun karbuwa a sassan duniya, matakin dake kara tabbatar da gudummawar da Sin ke bayarwa a fannin samar da ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi, kana wani bangare na gudummawar kasar ke bayarwa a yaki da matsalar sauyin yanayi .

Kasar Sin, kamar ragowar kasashe na da ikon zabar hanyoyin raya kanta bisa yanayin da take ciki, don haka, bunkasuwar kasar, kamar yadda ta sha nanatawa, har kullum buri da manufar kasar Sin, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallonta da ma yada jita-jitar cewa, wai ci gaban kasar Sin, musamman kokarin da take na zamanantar da kanta, baraza ce ga duniya.

A fili yake cewa, kasar Sin na da dabaru da fasahohi masu kyau a fannin ingiza zamanintarwa da hadin kan kasa da kasa, da sa kaimi ga canja salon makamashi, kuma dukkansu abin koyi ne ga kasashen duniya. Amma wasu kasashe na nuna kishi da ci gaban kasar Sin, inda suke kokarin yiwa wannan ci gaba bahaguwar fahimta tare da neman hana ci gabanta ta kowa ce hanya. Har kullum kasar Sin tana fatan kasashen yammacin duniya, za su kalli bunkasuwarta, da kokarin da take na zamanantar da kanta da idon basira, ta yadda za su dakatar da yada farfaganda maras tushe, ta daukar wannan manufa da masu fashin baki ke cewa, za ta amfani duniya, a matsayin wai barazana. Zakaran da Allah ya nufa da cara dai ko ana muzuru ko ana shaho sai ya yi. (Ibrahim Yaya)