logo

HAUSA

Matakan Sin na neman ci gaba mai inganci don cimma burin zamanintarwa

2024-01-24 08:53:32 CMG Hausa

Bayanai na nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya kammala shekarar 2023 da ci gaban da aka yi fatan cimmawa, duk da kalubalen cikin gida da matsin lamba daga waje, lamarin da ya ba da kwarin gwiwa ga tattalin arzikin duniya.

Hukumar kididdigar kasar ta nuna cewa, jimillar GDP na kasar Sin ya karu da kashi 5.2 bisa 100, adadin ci gaban ya fi abin da gwamnati ta yi hasashen samu na kusan kashi 5, kuma ya zarce kashi 3 cikin 100 a shekarar 2022.

Kasar Sin ta cimma manyan manufofin da aka sanya a gaba a shekarar 2023, kuma an samu ci gaba mai inganci, duk da matsaloli da kalubalen da suka kunno kai.

Gudummawar da kasar Sin ta bayar ga ci gaban GDPn duniya a shekarar 2023, ya kai sama da kashi 30 cikin 100, wanda ya zama injin din ci gaba mafi karfi a duniya. A wani bangare kuma, duk da koma baya a harkokin kasuwancin duniya, kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasashen waje sun karu a bara. Kididdigar farashin kayan masarufi, duk da hauhawar farashin kayayyaki a wasu kasashe, ta karu da kashi 0.2 cikin dari a bara.

Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a bana na da nasaba da yanayi masu kyau daban-daban, wadanda suka hada da ingantaccen yanayin tattalin arziki, da tsayin daka, da managartan matakai da kuzari mai karfi, da zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.

Masu sharhi na bayyana imanin cewa, ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci, da ci gaba da sa kaimi ga zamanintarwa irin ta kasar Sin, ko shakka babu za su kara samar da moriya ga duniya, da kara ba da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya. (Yahaya, Ibrahim/Sanusi Chen)