logo

HAUSA

Kasa da kasa sun yabi sakamakon tarihi da kasar Sin ya samu wajen kiyaye hakkin dan Adam

2024-01-24 14:16:40 CMG Hausa

Kasar Sin ta halarci taron nazarin hakkin dan Adam na kasa da kasa karo na hudu da kwamitin hakkin dan Adam na MDD ya gudanar a birnin Geneva na Switzerland a jiya Talata. Jakada Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva na kasar Switzerland da sauran kungiyoyin kasa da kasa, ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin kasar Sin don halartar taron.

Yayin taron, jakada Chen Xu ya gabatar da hanyoyin ci gaban hakkin dan Adam na kasar Sin da kuma babbar nasarar da aka samu, inda ya jadadda cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan mutunta da kiyaye hakkin dan Adam a matsayin muhimmin hanyar tafiyar da harkokin kasar, kuma tana tafiya kan wata hanyar ci gaban hakkin dan Adam da ta dace da zamani da kuma yanayin kasar.

Yayin nazarin, Sin ta sanar da matakan da za ta dauka guda 30 don kiyaye hakkin dan Adam, wadanda suka shafi inganta moriyar jama’a, karfafa kiyaye hakkin dan Adam ta hanyar dokoki, inganta hadin gwiwar hakkin dan Adam ta kasa da kasa, da nuna goyon baya ga tsarin hakkin dan Adam da sauransu.

Kasashen fiye da 120 sun yabi ci gaban aikin kiyaye hakkin dan Adam da kassar Sin ta samu, kuma sun yaba da kokarinta wajen inganta da kiyaye hakkin dan Adam, kamar sarrafa da gudanar da shirin hakkin dan Adam na kasa, kyautata dokokin iko da moriyar mata, ci gaba da kyautata tsarin tsaro da hidimomin zamantakewa na nakasassu. Sun yi imanin cewa, hanyar raya hakkin dan Adam da kasar Sin take bi ta dace da yanayin kasar da muradun jama'ar kasar, kana ta samar da wani sabon zabi ga sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa, su gudanar da bincike kan hanyar ci gaban hakkin dan Adam da kansu. (Safiyah Ma)