logo

HAUSA

Kayan da aka jigila cikin sauri a Sin ya alamta babban karfin tattalin arzikin kasar

2024-01-23 21:29:42 CMG Hausa

Alkaluman da gwamnatin kasar Sin ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa, gaba daya kwatankwacin adadin kayayyakin da aka saya ta yanar gizo da kuma jigilar su cikin sauri a kasar Sin a shekarar 2023, ya kai biliyan 132.07, adadin da ya karu da kaso 19.4 bisa dari a kan makamancin lokacin shekarar 2022, kuma ya kai matsayin koli a fadin duniya a cikin tsawon shekaru goma a jere. Wadannan kayayyakin da aka yi jigilar su cikin sauri sun hada da na cikin gida da kuma na ketare. An lura cewa, adadin ya karu cikin sauri matuka a cikin shekaru goma da suka gabata, kana adadin ya kai kaso 60 bisa dari cikin daukacin adadin kayayyaki a fadin duniya.

Shin mene ne yake sa kaimi ga ci gaban sha’anin jigilar kaya cikin sauri a kasar Sin? Hakika al’ummun Sinawa sun kai sama da biliyan 1 da miliyan 400, don haka kasar Sin ta kasance babbar kasuwa dake da babban boyayyen karfi a duniya, alkaluma sun nuna cewa, matsakaicin adadin kayayyakin da aka jigilar su a ko wace rana a kasar Sin ya kai miliyan 350, kuma kudin da Sinawa suka kashe kan sayayya ya ba da gudummowar kaso 82.5 bisa dari kan ci gaban tattalin arzikin kasar, inda karuwar tattalin arzikin kasar ta kai kaso 4.2 bisa dari sakamakon haka.

A halin da ake ciki yanzu, sana’ar jigilar kaya cikin sauri a kasar Sin ta riga ta kasance alamar ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. (Jamila)