logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya ba da umarnin fadada shirin ba da lamunin karatu ga dalibai don hada da bunkasa fasaha

2024-01-23 11:24:13 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula da asusun ba da lamuni na karatu ta Najeriya NELFUND da ta fadada shirin ta hanyar ba da rancen kudi mara ruwa ga daliban gida masu sha’awar shirye-shiryen bunkasa sana’o’i.

Tinubu ya ba da wannan umarni ne a fadar gwamnatinsa a ranar Litinin, inda ya ce, yana da matukar muhimmanci ga shirin ya hada da wadanda ba neman ilimin jami’a ba ne bukatarsu.

Ya bayyana cewa samun fasaha yana da mahimmanci "kamar yadda samun digiri na farko da na digiri na biyu ke da shi," yana mai jaddada mahimmancin baiwa matasan Najeriya dabarun aiki masu mahimmanci don samun nasara a ma'aikata na zamani.

Matakin fadada shirin ba da lamuni na dalibai domin bunkasa sana’o’i ya nuna yadda gwamnati ta yunkuro wajen magance bukatu na matasan kasar da kuma tabbatar da cewa sun shirya tsaf don fuskantar kalubale da damammaki da za su fuskanta a gaba. (Yahaya)