Mutane 16 ne suka mutu a hatsarin mota da ya auku a arewacin Najeriya
2024-01-23 10:24:44 CMG Hausa
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce akalla mutane 16 ne suka mutu bayan da wata motar bas ta kasuwa ta kutsa cikin wani rami da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, kwamandan hukumar kiyaye haddura ta tarayya a Kaduna, Kabir Nadabo, ya ce wasu mutane hudu sun jikkata a lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi.
Binciken da jami’an suka gudanar ya nuna cewa, hatsarin ya faru ne sakamakon kwacewa da motar ta yi a hannun direban a dalilin gudun wuce kima, a cewar Nadabo. Ya kara da cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin gwamnati.
Nadabo ya gargadi masu ababen hawa kan saba ka’idojin tuki, ya kuma bukaci sauran masu amfani da hanya, musamman masu ababen hawa, da su rika gargadin direbobin motocin kasuwa da su guji wuce gona da iri yayin da suke tuki. (Yahaya)