logo

HAUSA

Masana kimiyyar sirrai na Najeriya za su inganta kwayoyin hallittar amfanin gona

2024-01-23 09:58:16 CMG Hausa

Hukumar binciken aikin noma ta tarayyar Najeriya ARCN ta tabbatar da cewa, ta samu karin sabbin masana kimiyya har 1,650 da za su shigo cikin shirinta na karfafa bincike domin inganta kwayoyin halittar sirrai da dabbobi da ake da su a kasar.

Babban sakataren hukumar Farfesa Garba Sharubutu ne ya tabbatar da hakan a farkon wannan mako, lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Abuja game da nasarorin da hukumar ta samu a shekarar bara ta 2023.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Farfesa Garba Sharubutu ya ce, an sami wannan ci gaba ne na karin masanan bayan amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na samar da ingantattun irin shuka da za su taimaka wajen cimma burinta na wadata kasa da abinci a dan kankanan lokaci.

“Gwamnatin tarayyar ta amince a dauki masana kimiyya har 1,650 domin kara fadada yawan ma’aikatan da ake da su a bangaren binciken kimiyya, musamman ma wadanda za su kawo ci gaba a fannin inganta kwayoyin halittar irran shukarmu na gida.”

Babban sakataren ya ce abun da ake sa rai daga wadannan kwararrun masana dai shi ne amfani da iliminsu wajen bayar da gudummawa ga ci gaban cibiyoyin bincike da kwalejojin dake karkashin kulawar hukumar ta ARCN domin dai kyautata sha’anin samar da abinci a Najeriya.

Farfesa Garba Sharubutu ya jaddada bukatar samun tallafin cibiyoyin bincike na kasa da na kasashen waje domin dai bunkasa harkokin binciken noma da kuma tabbatar da wadatuwar abinci a kasa.

Ya sanar da cewa, a makonni biyu da suka gabata ma hukumar tasu ta samu nasarar fitar da sabbin nau’ikan irran shuka har guda 23 da aka gudanar da bincike a kansu a gidan Najeriya tare da hadin gwiwa da wasu hukumomin kasa da kasa.

A don haka ya yi kira ga manoman Najeriya da su rungumi amfani da sabbin irin shukar da aka samar saboda juriyarsu ga fari da kuma yawan ’ya’ya bayan girbi. (Garba Abdullahi Bagwai)