Ci Gaban Kasar Sin Zaburarwa Ce Ba Barazana Ba
2024-01-23 16:20:29 CMG Hausa
Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a jiya Litinin cewa, yaudarar cin zarafi da ’yan siyasar Amurka ke yi na kara tsanani. Wannan ya biyo bayan zargin da ’yan siyasar Amurka ke ci gaba da yadawa cewa, na'urorin fasahar sadarwa da batiran motoci masu amfani da wutar lantarki da kasar Sin ke kerawa, na barazana ga tsaron kasa.
Da alama dai, Amurka ta dage wajen ganin ta shafawa kasar Sin bakin fenti ta kowane hali. A baya, Amurka ta kasance mai juya kasashen duniya yadda ta ga dama saboda fa’idojin da take da su da fasahohin da ta mallaka, amma saurin ci gaban da kasa mai tasowa kamar Sin ta samu, bisa dukkan alamu, na tsone mata ido.
Ba tun a yau ’yan siyasar kasar suke yayata batun “barazana ga tsaron kasa” ba, amma har zuwa yau din, babu wata shaida ko hujja da ta tabbatar da zargin nasu. Maimakon haka, kiyayyar da Amurka ke yi da ci gaban kasar Sin ne ke kara fitowa bisa la’akari da yadda take dagewa wajen ganin ta dakile kasar Sin ta kowace hanya.
Hausawa kan ce “Wutsiyar rakumi ta yi nesa da kasa”. Kasar Sin ta yi nisa a fagen raya kanta cikin aminci ta hanyoyi daban-daban, kuma bisa dogaro da albarkatun da ta mallaka. Ci gaban kasar Sin da fasahohinta sun kasance abun zaburarwa da ma taimako ga kasashen duniya, har ita kanta Amurka.
A yanzu, ci gaban kasar Sin ya zama madogara da abun taimako ga kasashe masu tasowa domin ita ba ta kyashin ganin wani ya ci gaba, wanda daya ne daga cikin abun da Amurka ba ta son gani.
Sin kan raba fasahohinta ga kasashe masu tasowa bisa girmama juna kuma ba tare da sharadi ba, wanda shi ne abun da kasashe masu karamin karfi ke bukata na tada komadar tattalin arzikinsu. Shin wannan shi ne “barazana ga tsaron kasa”?
Idan har za a dauki raya kai da taimako a matsayin “barazana ga tsaron kasa” ban san me za a kira “tsoma baki cikin harkokin gida” da “yada jita-jita” da “yunkurin rarraba kawuna” ba, wadanda Amurka ke kan gaba wajen aiwatarwa.
Kamar yadda na fada a baya, ci gaban kasar Sin zaburarwa ce ga kasashen duniya, don haka kamata ya yi Amurka ta dauki darasi ta kuma yi kokarin lalubo hanyoyin raya kanta da kanta ba tare da mulkin mallaka ko ci da gumin wasu ba. Ko ba komai, kasar Sin ta nunawa duniya cewa, akwai hanyoyin samun ci gaba cikin aminci da lumana.(Fa’iza Mustapha)