logo

HAUSA

Taron kolin kungiyar kasashe 'yan ba ruwanmu

2024-01-22 16:29:28 CMG

Taron kolin kungiyar kasashe ‘yan ba ruwanmu karo na 19 ke nan da aka kammala a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda. Sanarwar Kampala da aka zartas a wajen taron ta yi kira da a kiyaye tsarin cudanyar bangarori daban daban da ma karfafa tasirin kungiyar a harkokin duniya, a wani kokari na samar da zaman lafiya da adalci da albarka a duniya.