logo

HAUSA

Taron kolin kasashen kudancin duniya karo na 3 ya yi kira da a sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na duniya

2024-01-22 10:06:02 CMG

A jiya Lahadi ne aka bude taron kolin kasashen kudancin duniya ko “South Summit” karo na 3, inda shugabannin kasashen kudancin duniya suka yi kira da a sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na duniya, wanda suke ce rashin adalci ne ga kasashe masu tasowa.

Taron na kwanaki biyu, ana gudanar da shi ne a karkashin taken “Kar a Bar Kowa a Baya” kuma ana sa ran zai kawo wani sabon salo na hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobinta 134. Taron kasashen kudu, shi ne hukumar da ke yanke shawara kan harkoki na kungiyar G77, wanda aka kafa a watan Yunin 1964.

Salvador Valdes Mesa, mataimakin shugaban kasar Cuba, kuma shugaban kungiyar G77 mai barin gado, ya ce an kira taron ne a daidai lokacin da kasashe masu tasowa ke fuskantar kalubale masu sarkakiya a harkokin duniya.

Mesa ya bukaci kasashe mambobin kungiyar da su kasance masu hadin kai wajen mayar da martani ga tsarin tattalin arzikin duniya mara adalci a halin yanzu.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar G77 mai jiran gado, ya ce dole ne kungiyar ta dage wajen nema ma kasashe mambobinta adalci a tsarin hada-hadar kudi na duniya. (Yahaya)