logo

HAUSA

Chen Qin: Na shaida yadda matasan kasar Sin ke kara sha'awar al'adun gargajiyar kasar

2024-01-22 16:04:19 CMG Hausa

A cikin 'yan shekarun nan, dalibai 'yan kasar Sin da ke karatu a kasashen ketare da yawa suna zabar komawa kasarsu don ba da gudummawarsu ga ci gaban kasa, tare da tabbatar da burikansu, da kuma kokartawa wajen cimma su. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani labari ne game da yadda wata baiwar Allah mai suna Chen Qin ke raya sana’arta.

Chen Qin ta kammala karatunta ne a kwalejin koyar da kade-kade da wake-wake ta birnin Xi'an dake kasar Sin da jami’ar Birmingham City ta kasar Birtaniya, inda a halin yanzu malama ce mai koyar da wasan kayan goge na Pipa, kuma mai yada labarai a shafin sada zumunta na yanar gizo, inda mabiyanta suka zarce 300,000.

“Na fara koyon wasa da Pipa tun ina ‘yar shekara tara, kuma ya zuwa yanzu na yi shekaru 29 ina wasa da Pipa.”

Yayin da take karatu a kasashen waje, Chen Qin da wasu mawaka da dama sun kafa wata kungiyar makada mai suna "BCCM". Birmingham shi ne birni na biyu mafi girma a Burtaniya. A wancan lokacin, kungiyar ta gudanar da wani bikin kide-kide a dakin wasan kide-kide dake tsakiyar birnin. A wannan dare da aka yi ruwan sama, masu kallo sun yi dogon layi tun daga bakin kofar dakin wasan har zuwa dayan bangaren titin.

“Fiye da mutane 600 ne suka zo dakin kide-kide, wanda ke iya daukar mutane 500. Lokacin da muka yi wakar ‘Zuriyar Dodanniya’. A karshe, dukkan masu sauraro sun tashi tsaye suna rera waka tare da mu, a wannan lokacin, ba za a iya kwatanta girma da hadin kan al’ummar kasar Sin da ake ji ba. Akwai wani dattijo dan Biritaniya da mai yiwuwa bai fahimci ma’anar kalmomin dake cikin wakar ba, amma ya rera waka tare da mu da babbar murya, ba zan iya mantawa da shi ba. Ina tsaye a kan dandalin, hawaye na zubo min, ni ‘yar kasar Sin ce kuma ina alfahari da kasata!”

Chen Qin ta ce, a lokacin da take karatunta a kasashen waje, ta lura da yadda matasa Sinawa da dama dake wurin ke gabatar da al'adu da fasahar gargajiyar kasar Sin ta hanyoyi daban-daban, domin kowa yana fatan mutane da yawa za su san wadannan taskokin na kasar Sin.

“A zamanin yau, a kan tituna a kasashen waje, an saba ganin jama’a na raye-rayen kasar Sin, da wasan kungfu da kuma wasan kayan goge na guzheng na kasar Sin. Ni ma na taba buga Pipa a titin kasar Burtaniya a baya, amma bai yi tasiri sosai ba, saboda ba a samu ci gaba sosai a lokacin ba. Yanzu, a cikin yanayin da bayanai ke saurin yaduwa, muna iya yin kyakkyawar mu’amala ta yanar gizo da kuma a zahiri. Ina tsammanin daliban kasashen duniya za su iya taka rawar gani, kuma ayyukan yada al’adu na gado suna da mahimmanci.”

Rayuwar Chen Qin na karatu a Burtaniya ya bude idanunta, kuma ya ba ta kwarin gwiwa sosai. Bayan ta dawo daga karatu a kasashen waje, Chen Qin ta gano cewa, wasu mutane ko kuma kungiyoyi na sha’awar wallafawa da raba bayanai ta hanyar kasidu, bidiyo, sauti da sauransu ta hanyar yanar gizo, ta yadda za su iya samun kudin shiga, irin sana’ar dake samun saurin bunkasuwa ke nan a kasar Sin. Ta ce irin yanayin da ake ciki ya kunna mata sha'awar gudanar da kasuwanci.

Yanzu, ta ce ta kasance baliga a wannan fanni. A cikin fiye da shekaru hudu, ta tara magoya baya fiye da dubu 30.

“A matsayina na mai aikin watsa labaru mai zaman kanta, ina kuma son in gabatar da ilimi ga dukkan masu kallo a yanar gizo, ta yadda kowa zai iya ganin ruhin al'adun kasar Sin, wanda ya kasance asalinmu mai cike da imani. Misali, ta yaya kayan goge na Pipa ya kasance a Daular Song? Yaya Pipa ya kasance a Daular Tang? Idan aka zo batun tarihi da asalin Pipa, mutane da yawa ba su da ilimi sosai a wannan bangare. Ina amfani da wannan hanyar da mutane suke so wajen yada al’adunmu na gargajiya. A gani na, aikin na da ma’ana sosai.”

Chen Qin ta ce, tana jin cewa matasa suna kara sha'awar al'adun gargajiya na kasar Sin. Yawancin masoyanta matasa ne, kuma yanzu tana koyawa yara da dama wasan Pipa. Ta ce, tana fatan ta hanyar kokarinta, karin matasa za su fahimci ma’anar al'adun kasar Sin, da kuma nuna kyawawan al'adu kasar Sin ga duniya.

“Dangane da gadon al'adun gargajiya, a zahiri kasarmu ta dade tana gudanar da jerin ayyukan rayasu. Misali, lokacin da nake makarantar koyar da fasaha, na san cewa kasarmu ta kafa gidauniyar fasaha ta kasa don ba da tallafi na musamman ga masu kirkira da magada al’adun gargajiya. Na gaskata cewa muddin mutane suka yayata al’adun gargajiya na kasarmu, to lallai wani zai koya daga gare su. Zuriyoyi masu zuwa, su ne fatanmu a wannan fannin."

Da take magana kan ayyukan kirkire-kirkire a nan gaba, Chen Qin na fatan tsayawa kan ainihin manufarta kan hanyar bunkasa al'adun gargajiya, da kuma ba wa duniya labaran ban mamaki na al'adun gargajiya na kasar Sin. Ta ce,

“Yanayin cikin gida yana da kyau sosai, kuma na yi imanin cewa, mutane da yawa za su iya fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin a nan gaba. A nan gaba, ina fatan yada muryarmu a duk fadin duniya ta hanyar ayyukanmu. Yin hakan, ko a gida ko a waje, yana da kyau sosai kuma zai yi tasiri mai kyau a duniya. Za mu yi kokari don karfafawa da kuma bunkasar wannan aiki.”