logo

HAUSA

An kaddamar da aikin ginin rukunin gidaje 1,500 a jihar Jigawa ta Najeriya

2024-01-22 09:11:17 CMG Hausa

Ministan tsaro na tarayyar Najeriya Mahammadu Badaru Abubakar ya jagoranci kaddamar da aikin ginin rukunin gidaje 1,500 a birnin Dutse da wasu manyan garuruwa 7 dake jihar.

Ministan ya bayyana aikin ginin a matsayin mafita da za ta kawo karshen matsalolin muhalli da ake fuskanta a jihar, wanda wannan kamar yadda ya ce ya zo daidai da kudurce-kudurcen shugaban kasa na saukaka hanyoyin mallakar muhalli ga ’yan kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Garuruwan da za su amfana daga wadannan gidaje 1,500 da za a gina sun hada da Hadeja, Kazaure, Ringim, Birnin Kudu, Babura da Kafin Hausa.

Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana cewa, babu shakka samar da gidajen zai kara kyautata yanayin rayuwa a jihar baki daya, sanann kuma tattalin arzikin jihar zai kara ingantuwa kasancewar kayayyakin da za a gudanar da aikin ginin da kuma leburorin da za su gudanar da aikin duk a jihar za a samar da su.

Ya bayyana gwamnan jihar ta Jigawa a matsayin shugaba mai hangen nesa wanda a ko yaushe yake kokarin ganin ya bar wani abun tarihi ga gwamnatinsa.

Da yake jawabi, gwamnan jihar ta Jigawa Malam Umar Namadi ya ce, samar da gidaje guda 1,500 yana daya daga cikin ajandoji 12 da gwamnatinsa ta zo da su da za su taimaka wajen raya manyan biranen dake jihar Jigawa.

Gwamnan ya ce, aikin ginin yana da riba ne guda uku wadanda suka hada da wadata al’umma da ingantaccen muhalli, samar da aikin yi da kuma kyautata sha’anin tattalin arzikin al’ummar jihar baki daya.

“Za mu yi kokarin ganin cewa, mun samar da gidaje masu rangwamen farashi da saukin mallaka ga al’ummar jihar Jigawa, wannan yana daga cikin alkawuran da na dauka yayin yakin neman zabe da kuma kokarinmu na hidimtawa al’ummar jihar wanda duka suna cikin sabon shirinmu na ci gaban jihar Jigawa.” (Garba Abdullahi Bagwai)