logo

HAUSA

Ba irin wannan Amurkar kasashen yankin gabas ta tsakiya suke bukata ba

2024-01-22 16:16:18 CMG Hausa

“A yankin gabas ta tsakiya, na ji kusan kowace kasa na cewa, tana bukatar Amurka, tana bukatarmu a wajen……Tana bukatar jagorancinmu.”

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Anthony Blinken ke nan ya fadi haka a lokacin da ya halarci taron dandalin tattalin arzikin duniya da ya gudana a kwanan nan a birnin Davos na kasar Switzerland, kalaman da suka janyo dariya daga masu bibiyar shafukan kafofin sada zumunta na kasar Amurka, inda a shafin kafar X, suka bayyana cewa, “A’a, ba su bukata” “Amurka tuni ta ci amanarta” “Babu wanda ke bukatar sojojin mamaya na Amurka da hare-harenta”……

Kwanaki sama da 100 ke nan tun bayan barkewar rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, lamarin da ya haifar da ci gaban tabarbarewar yanayin jin kai a yankin, rikicin da har ya tsananta halin da ake ciki a Bahar Maliya. A farkon wannan wata, Mista Blinken ya ziyarci kasashen yankin gabas ta tsakiya da dama, karkashin sunan daidaita rikici tsakanin Palasdinu da Isra’ila, sai dai a yayin ziyararsa, kusan Isra’ila ba ta taba daina hare-harenta a zirin Gaza ba, bayan ziyararsa kuma, sassan yankin na gabas ta tsakiya sai kara tsumduma cikin kazamin fada suka yi.

A hakika, tun bayan barkewar rikicin, ba ma kawai Amurka ta kara tura sojojinta zuwa yankin gabas ta tsakiya ba, har ma ta kara bayar da gudummawar soja ga kasar Isra’ila. A watan Disamban bara, sau biyu gwamnatin kasar Amurka ta sayar da makamai cikin gaggawa ga Isra’ila ba tare da samun amincewar majalisar dokokin kasar ba. Ban da haka, Amurka ta sha kawo cikas ga kokarin da ake yi na kwantar da kurar rikicin, sakamakon yadda ta kada kuri’ar rashin amincewa da kudurin tsagaita bude wuta da aka gabatar a gun kwamitin sulhun MDD.

Babu wani abu da Amurka ke kawo wa kasashen gabas ta tsakiya da ma sauran sassan duniya, illa dai yake-yake da tashin hankali da ma dakushewar tattalin arziki, sakamakon yadda take da niyyar kiyaye babakeren da ta kafa a duniya da moriyar siyasa na cin mummunar riba daga cinikin makaman soja da take yi.

In mun duba tarihin kasar na sama da tsawon shekaru 240, shekaru 16 ne kawai ba ta yaki. Da Afghanistan da Iraki da Syria da Libya da Ukraine da ma Palasdinu, tashin hankalin da ke addabar kasashe da yankuna da dama sun auku ne sakamakon kasar Amurka. Ban da haka, Amurka tana kuma dukufa a kan yayata tsare-tsarenta a duniya, inda ta sa kaimin juyin juya hali a kasashe da dama, sai dai salon dimokuradiyyarta bai dace da yanayin da kasashen da ta tilasta ma ba, matakin da ya sa suke fuskantar lalacewar harkokin siyasa da tsari. Ga kuma yadda ta yi ta kara kudin ruwa na dalarta yadda ta ga dama don kwashe ribar tattalin arzikin kasa da kasa, lallai yadda take tsananin son kai ya wadatar da kanta, amma ya lalata tsarin tattalin arzikin duniya da ma tsarin dokokin hukumar cinikayyar duniya, haka kuma ya dakile farfadowar tattalin arzikin duniya.

Amurka, tuni ta zama mafarin tashin hankali na duniya.

Ba irin wannan Amurkar kasashen yankin gabas ta tsakiya suke bukata ba, ballantana ma sauran kasashen duniya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)