logo

HAUSA

Firaministan Isra’ila ya yi watsi da shirin tsagaita bude wuta yayin da sojoji suka ci gaba da kai farmaki a Gaza

2024-01-22 11:23:08 CMG

Firaministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a jiya Lahadi ya yi watsi da shawarar yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kasashen Qatar, Amurka da Masar suka gabatar, yayin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da lugudan wuta kan yankin Falasdinu.

Rahoton jaridar Wall Street Journal ya rawaito daga jami’an Masar a ranar Lahadi cewa, masu shiga tsakanin sun gabatar da shirin tsagaita wuta na kwanaki 90 kamar haka. A mataki na farko za a daina yaki, kuma Hamas za ta saki dukkan fararen hular Isra’ila da take tsare da su, yayin da Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinu tare da kara kai agaji. Shirin ya kuma hada da sake gina Gaza da tattaunawa don tsagaita bude wuta na dindindin da kuma sake kaddamar da tsarin kafa kasar Falasdinu.

Netanyahu ya yi watsi da muhimman abubuwan da ke cikin shirin, ciki har da batun kafa kasar Falasdinu. "Ba zan yi kasa a gwiwa ba kan cikakken ikon tsaron Isra'ila na mamaye dukkan yankunan yammacin kogin Jordan," a cewar shi a cikin wani jawabin da ya yi wa al'ummar kasar ta kafar bidiyo. Yankin yammacin gabar kogin Jordan, yanki ne da Isra'ila ta kwace tare da zirin Gaza a yakin Gabas ta Tsakiya na shekarar 1967. 

Kalaman sun kasance tamkar kin amincewa da kiraye-kirayen neman diyaucin Falasdinu ne bayan tattaunawa da shugaban Amurka Joe Biden kan makomar Gaza bayan yakin. Netanyahu ya ce ya tattauna da Biden ta wayar tarho a karshen mako kuma "na jaddada aniyarmu ta cimma dukkan manufofin yakin," ciki har da kawar da Hamas.  (Yahaya)