Sin Na Taka Rawar Gani Wajen Inganta Dunkulewar Duniya Da Kyautata Cinikayyar Kasa Da Kasa
2024-01-22 16:50:22 CMG Hausa
Idan har da gaske ake son a ciyar da duniya gaba, to hadin gwiwar siyasa da tattalin arziki, da hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire da inganta kwararrun masana'antu na kasa da kasa sun zama wajibi don tunkarar hadarin kenkene kasuwanci ta hanyar sanya takunkumi, da gurbacewar muhalli, da rikice-rikicen tattalin arziki, da rugujewar tsarin samar da kayayyaki a duniya. Kana, karfafa amincewa da juna yayin hadin gwiwa don shawo kan wadannan kalubalolin na da matukar muhimmanci.
Domin ba da shawara game da yadda za a tunkari wadannan matsalolin, Firaministan kasar Sin Li Qiang ya halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya (WEF) na shekarar 2024 da aka gudanar a Davos, ya kuma gabatar da muhimmin jawabi a ranar 16 ga wannan wata, kasancewar kasar Sin a gun taron ya nuna cewa, a shirye take ta ci gaba da taka rawar gani, wajen inganta hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa da kuma tunkarar matsalolin duniya.
Yunkurin da kasar Sin ta yi kan muhimmancin ra'ayin bangarori daban-daban ya ba da tabbacin cewa gudummawar da take bayarwa na ciyar da bil'adama gaba. A cikin shawarwarin da firaministan ya gabatar, ya yi kira da a daidaita manufofin tattalin arziki, da inganta kwararrun masana'antu na kasa da kasa, da hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, da hadin gwiwa a fannin raya koren muhalli, da hadin gwiwa tsakanin sassan duniya, yayin da ya jaddada aminci tsakanin shugabannin kasashen duniya.
Baya ga zaman lafiya da ci gaban kasar Sin, ba shakka kasashen duniya suna sa ido kan irin gudummawar da kasar Sin ke bayarwa wajen kara tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya. Kamar yadda Okonjo-Iweala, babbar darektar hukumar cinikayya ta duniya (WTO) ta ce a gefen taron dandalin tattaunawar tattalin arzikin duniya da aka gudanar a Davos, yayin da take bayyana muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa wajen habaka cinikayyar duniya da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya, "Duk abin da ya faru da kasar Sin yana yin tasiri ga duniya, hakan ya sanya taka rawar ganin tattalin arzikin kasar Sin ya kasance maslahar kowa da kowa."
La’akari da taken dandalin tattaunawar tattalin arziki na duniya na 2024 wato "karfafa amincewa" wanda ya jaddada sauke nauyi, da bude kofa, da daidaita gibi tsakanin kasashe masu tasowa da masu ci gaba, da daidaito don jaddada amincewa da juna yayin da ake warware matsalolin duniya kamar sauyin yanayi, rikice-rikicen shiyya-shiyya, da ci gaban kirkirarriyar basira wato AI, da ingancin tsarin samar da kayayyaki a duniya da farfado da tattalin arziki duk suna dogaro ne ga kwarin gwiwa da aminci tsakanin kasashe masu tasowa da ma masu ci gaba.
Dole ne dandalin na WEF ya zama kafa mai samar da sauki ga hada-hadar kasuwanci a duniya da kuma kawar da shingayen cinikayya, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki. Kasar Sin za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan inganta dunkulewar duniya da manufar dandalin WEF ta cire shingaye daga cinikayyar kasa da kasa. (Muhammed Yahaya)